YouVersion Logo
Search Icon

Amos 9

9
Ba a Kauce wa Hukuncin Allah
1Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce,
“Bugi ginshiƙan Haikali don shirayi
duka yă girgiza.
Farfasa su, su fāɗi a kan mutane!
Sauran mutane kuwa,
Zan kashe su a wurin yaƙi.
Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.
2Ko da za su nutsa zuwa lahira,
Zan kama su.
Ko sun hau Sama,
Zan turo su.
3Ko da za su hau su ɓuya a bisa
ƙwanƙolin Dutsen Karmel,
Zan neme su in cafko su.
Ko da za su ɓuya mini a ƙarƙashin
teku,
Sai in sa dodon ruwa yă yayyage su.
4Idan kuwa abokan gābansu ne suka
kama su,
In umarce su su hallaka su da
takobi,
Tun da na yi ƙudurin ƙare su.”
5Ubangiji Allah Mai Runduna
Ya taɓi duniya, ta girgiza.
Duk waɗanda suke zaune cikinta
Suna baƙin ciki.
Duniya duka takan hau
Ta kuma gangara kamar ruwan
Kogin Nilu.
6Ubangiji ya gina al'arshinsa a sama,
Ya shimfiɗa samaniya a bisa duniya.
Ya sa ruwan teku ya zo,
Ya kwarara shi a bisa duniya.
Sunansa Ubangiji ne!
7Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila,
Ina yi da ku daidai yadda nake yi da
Habashawa.
Na fito da Filistiyawa daga Kaftor,
Suriyawa kuwa daga Kir,
Daidai yadda na fito da ku daga
Masar.
8Ina dai kallon mulkin nan mai zunubi.
Zan hallaka su daga duniya,
Amma ba zan hallaka dukan jama'ar
Yakubu ba.
9“Zan umarta a rairayi jama'ar Isra'ila
Da matankaɗi kamar hatsi.
Zan rairaye su daga cikin sauran
al'umma,
Duk da haka ko ƙwaya ɗaya ba za
ta salwanta ba.
10Masu zunubi daga cikin jama'ata za
su mutu a yaƙi,
Wato dukansu da suke cewa,
‘Allah ba zai bar wata masifa ta
kusace mu ba!’ ”
Ceton da Za a Yi wa Isra'ila Nan Gaba
11 # A.M 15.16-18 “Wata rana zan sāke tayar da birnin
Dawuda
Tankar yadda akan ta da gidan da ya
rushe.
Zan gyara garunsa, in sāke mai da
shi.
Zan sāke gina shi in mai da shi
kamar yadda yake tun dā.
12Ta haka jama'ar Isra'ila za ta ci
nasara bisa sauran ƙasar Edom
wadda ta ragu,
Da bisa dukan al'umman da a dā su
nawa ne,”
In ji Ubangiji, wanda zai sa
al'amarin ya auku.
13Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna
zuwa,
Sa'ad da girbi zai bi bayan huda nan
da nan,
Matsewar ruwan inabi kuma
Za ta bi bayan shuka nan da
nan.
Duwatsu za su zubo da ruwan inabi
mai zaƙi,
Tuddai kuma su gudano da shi.
14Zan komo da mutanena ƙasarsu,
Za su giggina biranensu da suka
rurrushe,
Su zauna a cikinsu.
Za su shuka gonakin inabi, su sha
ruwan inabin.
Za su yi lambuna, su ci amfaninsu.
15Zan dasa su a ƙasar da na ba su,
Ba kuwa za a ƙara tumɓuke su
ba.”
Ubangiji Allahnku ne ya faɗa.

Currently Selected:

Amos 9: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in