Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna
zuwa,
Sa'ad da girbi zai bi bayan huda nan
da nan,
Matsewar ruwan inabi kuma
Za ta bi bayan shuka nan da
nan.
Duwatsu za su zubo da ruwan inabi
mai zaƙi,
Tuddai kuma su gudano da shi.
Zan komo da mutanena ƙasarsu,
Za su giggina biranensu da suka
rurrushe,
Su zauna a cikinsu.
Za su shuka gonakin inabi, su sha
ruwan inabin.
Za su yi lambuna, su ci amfaninsu.