Amos 9:13-14
Amos 9:13-14 HAU
Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna zuwa, Sa'ad da girbi zai bi bayan huda nan da nan, Matsewar ruwan inabi kuma Za ta bi bayan shuka nan da nan. Duwatsu za su zubo da ruwan inabi mai zaƙi, Tuddai kuma su gudano da shi. Zan komo da mutanena ƙasarsu, Za su giggina biranensu da suka rurrushe, Su zauna a cikinsu. Za su shuka gonakin inabi, su sha ruwan inabin. Za su yi lambuna, su ci amfaninsu.