YouVersion Logo
Search Icon

Amos 8

8
Wahayi na Huɗu, Kwandon Ɓaure na Ci
1Ubangiji ya nuna mini wahayi, sai na ga kwandon ɓaure na ci. 2Sai Ubangiji ya ce, “Amos, me ka gani?”
Na ce, “Kwandon ɓaure na ci.”
Ubangiji kuma ya ce mini, “Ƙarshen jama'ata Isra'ila ya zo. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba. 3Waƙoƙin da akan raira a fāda, za su zama na makoki a wannan rana. Za a iske gawawwaki ko'ina. Ba za a ji motsin kome ba.”
An kai Ƙarshen Isra'ila
4Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata, kuna ƙoƙari ku hallakar da matalautan ƙasar.
5Kuna ce wa kanku, “Mun ƙosa
keɓaɓɓun kwanakin nan su wuce,
Mu sami damar yin kasuwancinmu.
Yaushe Asabar ɗin za ta ƙare ne?
Ko mā sami damar kai hatsinmu
kasuwa,
Mu sayar musu da tsada,
Mu yi awo da ma'aunin zalunci,
Mu daidaita ma'auni yadda za mu
cuci mai saya?
6Za mu sayi matalauci da azurfa ya
zama bawa,
Mai fatara kuma da takalma
bi-shanu.
Za mu sayar da ruɓaɓɓen hatsi,
Mu ci riba mai yawa.”
7Ubangiji Allahn Isra'ila ya riga ya
rantse,
Ya ce, “Ba zan manta da mugayen
ayyukanku ba.
8Shi ya sa ƙasar za ta girgiza,
Duk wanda yake cikinta zai yi baƙin
ciki.
Ƙasa duka za ta girgiza.
Za ta hau ta sauka kamar Kogin Nilu.
9A wannan lokaci rana za ta fāɗi da
tsakar rana,
Duniya ta duhunta da rana kata.
Ni, Ubangiji ne na faɗa.
10Zan mai da bukukuwanku makoki,
In sa waƙoƙinku na murna su zama
na makoki.
Zan sa muku tufafin makoki,
In sa ku aske kanku.
Za ku yi makoki kamar iyayen da
suka rasa tilon ɗansu.
Ranan nan mai ɗaci ce har ƙarshe.
11“Lokaci yana zuwa da zan aiko da
yunwa a ƙasar.
Mutane za su ji yunwa,
Ba ta abinci ba,
Za su ji ƙishi,
Ba na ruwa ba.
Za su ji yunwar rashin samun saƙo
daga wurin Ubangiji.
Ni Ubangiji ne, na faɗa.
12Mutane za su raunana, su riƙa kai
da kawowa,
Daga gabas zuwa yamma, daga
kuma kudu zuwa arewa.
Za su dudduba ko'ina suna neman
saƙo daga Ubangiji,
Ba kuwa za su samu ba.
13A ranan nan kyawawan 'yan mata
da samari
Za su faɗi saboda ƙishirwa.
14Waɗanda suka yi rantsuwa da
gumakan Samariya,
Waɗanda suka ce, ‘Na rantse da
gunkin Dan,
Da ran gunkin Biyer-sheba,’
Irin waɗannan mutane za su fāɗi,
Ba za su ƙara tashi ba.”

Currently Selected:

Amos 8: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in