YouVersion Logo
Search Icon

Oba 1

1
Ƙasƙancin Edom
1Annabcin Obadiya ke nan.
Wannan shi ne abin da Ubangiji Allah ya ce a kan al'ummar Edom.
Ubangiji ya aiki manzonsa wurin
sauran al'umma,
Mun kuwa ji saƙonsa cewa,
“Ku zo! Mu tafi mu yi yaƙi da
Edom!”
2Ubangiji ya ce wa al'ummar Edom,
“Zan maishe ki ƙanƙanuwa a cikin
sauran al'umma,
Za a raina ki ƙwarai.
3Girmankanki ya yaudare ki,
Kina zaune a kagara, a kan dutse,
Wurin zamanki yana can
ƙwanƙolin duwatsu.
Don haka a zuciya kike cewa,
‘Wa zai saukar da ni ƙasa?’
4Ko da yake kina shawagi can sama
kamar gaggafa,
Gidanki kuma yana can cikin taurari,
Daga can zan saukar da ke,” in ji
Ubangiji.
5“Idan ɓarayi sun shiga gidanki,
Idan kuma 'yan fashi sun shiga
gidanki da dare,
Yaya za su washe ki?
Za su sace abin da ya ishe su ne
kaɗai,
Idan kuma ɓarayin 'ya'yan inabi
sun shiga gonar inabinki,
Za su bar miki kala kurum.
6Isuwa, wato Edom, ga taskarka,
An washe ta ƙaƙaf!
7Waɗanda kake amana da su,
Za su kore ka daga ƙasarka.
Mutanen da suke amana da kai,
Za su yaudare ka,
Su ci ka da yaƙi.
Abokan nan naka da kake ci tare da
su za su kafa maka tarko,
Sa'an nan su ce, ‘Ina dukan wayon
nan nasa?’ ”
8Ni Ubangiji na ce, “A ranar da zan
hukunta Edom,
Zan hallaka masu hikimarka,
Zan shafe hikima daga dutsen
Isuwa.
9Jarumawanka za su firgita, ya
Teman,
Za a kashe kowane mutum daga
dutsen Isuwa.
10“Saboda kama-karyar da ka yi wa
Yakubu ɗan'uwanka,
Za a sa ka ka sha kunya,
Za a hallaka ka har abada.
11A ranan nan ka tsaya kawai,
A ranar da abokan gāba suka fasa
ƙofofinsa.
Suka kwashe dukiyarsa,
Suka jefa kuri'a a kan Urushalima.
Ka zama kamar ɗaya daga cikinsu.
12Ba daidai ba ne ka yi murna
Saboda wahalar da ta sami
ɗan'uwanka.
Ba daidai ba ne ka yi farin ciki
Saboda halakar mutanen Yahuza.
Ba daidai ba ne ka yi musu dariya
A ranar wahalarsu.
13Ba daidai ba ne ka shiga ƙofar
jama'ata
A ranar da suke shan masifa.
Ba daidai ba ne ka yi murna
A kan bala'in ɗan'uwanka.
Ba daidai ba ne ka washe dukiyarsa
A ranar masifarsa.
14 # Ish 34.5-17; 63.1-6; Irm 49.7-22; Eze 25.12-14; 35.1-15; Amos 1.11,12; Mal 1.2-5 Ba daidai ba ne ka tsaya a mararraba,
Don ka kashe waɗanda suke ƙoƙarin
tserewa.
Ba daidai ba ne ka ba da waɗanda
suka tsere a hannun maƙiyansu
A ranar wahala.”
Hukuncin Al'ummai
15“Ranar da ni Ubangiji zan
shara'anta al'ummai duka ta zo
kusa,
Ke, Edom, abin da kika yi,
Shi ne za a yi miki.
Ayyukanki za su koma a kanki.
16Kamar yadda kuka sha hukunci a
kan tsattsarkan dutsena,
Haka dukan sauran al'umma za su yi
ta sha.
Za su sha, su yi tangaɗi,
Su zama kamar ba su taɓa kasancewa
ba.”
Cin Nasarar Isra'ila
17“Amma za a sami waɗanda za su
tsira daga Dutsen Sihiyona,
Dutsen zai zama wuri ne mai tsarki.
Jama'ar Yakubu za ta mallaki
mallakarta.
18Jama'ar Yakubu za ta zama kamar
wuta,
Jama'ar Yusufu kuwa kamar
harshen wuta,
Jama'ar Isuwa za ta zama kamar
tattaka.
Za su ƙone ta, su ci ta, ba wanda zai
tsira.
Ni Ubangiji na faɗa.”
19Isra'ilawan da yake Negeb za su
mallaki dutsen Isuwa,
Waɗanda suke a filaye na Yahuza za su
mallaki ƙasar Filistiya.
Isra'ilawa za su mallaki yankin
ƙasar Ifraimu da Samariya,
Jama'ar Biliyaminu za su mallaki
Gileyad.
20Rundunar masu zaman talala na
Isra'ilawa
Za su mallaki Kan'aniyawa har zuwa
Zarefat.
Masu zaman talala na Urushalima da
suke a Sefarad
Za su mallaki biranen Negeb.
21Isra'ilawa za su hau Dutsen
Sihiyona, su cece shi,
Za su mallaki dutsen Isuwa,
Ubangiji ne Sarki.

Currently Selected:

Oba 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in