A.M 6
6
Zaɓen Mutum Bakwai Masu Hidima
1To, a kwanakin nan da yawan masu bi suke Ƙaruwa, sai Yahudawa masu jin Helenanci suka yi wa Ibraniyawa gunaguni domin bā a kula da matayensu waɗanda mazansu suka mutu, a wajen rabon gudunmawa a kowace rana. 2Sai goma sha biyun nan suka kirawo duk jama'ar masu bi, suka ce, “Ai, bai kyautu ba mu mu bar wa'azin Maganar Allah, mu shagala a kan sha'anin abinci. 3Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku, waɗanda ake yabawa, cike da Ruhu da kuma hikima, waɗanda za mu danƙa wa wannan aiki. 4Mu kuwa sai mu nace da yin addu'a da kuma koyar da Maganar.” 5Abin da suka faɗa kuwa ya ƙayatar da jama'a duka. Sai suka zaɓi Istifanas, mutumin da yake cike da bangaskiya da Ruhu Mai Tsarki, da Filibus, da Burokoras, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da Nikolas mutumin Antakiya wanda dā ya shiga Yahudanci. 6Waɗannan ne aka gabatar a gaban manzannin. Bayan sun yi addu'a kuma, suka ɗora musu hannu.
7Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ta ƙaruwa yake yi ƙwarai da gaske, firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na'am da bangaskiyar nan.
An Kama Istifanas
8To, Istifanas, cike da alheri da iko, ya yi ta yin manyan al'ajabai da mu'ujizai a cikin jama'a. 9Sa'an nan waɗansu na majami'ar da ake kira majami'ar Libartinawa, wato Kuraniyawa da Iskandariyawa, da kuma waɗansu daga ƙasar Kilikiya da ta Asiya, suka tasar wa Istifanas da muhawwara. 10Amma ko kaɗan ba dama su yi masa mūsu, domin ya yi magana da hikima, Ruhu na iza shi. 11Sai suka zuga mutane a asirce, su kuwa suka ce, “Mun ji shi yana zagin Musa, yana saɓon Allah.” 12Ta haka suka ta da hankalin jama'a, da shugabanni, da malaman Attaura, su kuma suka aukar masa, suka kama shi, suka kawo shi a gaban majalisa. 13Sai suka gabatar da masu shaidar zur, suka ce, “Mutumin nan ba ya rabuwa da kushe tsattsarkan wurin nan, da kuma Attaura, 14don mun ji shi yana cewa wai wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan, yă kuma sauya al'adun da Musa ya bar mana.” 15Da duk waɗanda suke zaune a majalisar suka zura masa ido, suka ga fuska tasa kamar fuskar mala'ika take.
Currently Selected:
A.M 6: HAU
Highlight
Share
Copy
![None](/_next/image?url=https%3A%2F%2Fimageproxy.youversionapi.com%2F58%2Fhttps%3A%2F%2Fweb-assets.youversion.com%2Fapp-icons%2Fen.png&w=128&q=75)
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979