A.M 5
5
Hananiya da Safiratu
1Amma wani mutum mai suna Hananiya, da mata tasa Safiratu, ya sayar da wata mallaka tasa, 2sai ya ɓoye wani abu daga cikin kuɗin, da sanin matarsa, ya kawo sashin kuɗin kurum ya ajiye a gaban manzanni. 3Sai Bitrus ya ce, “Kai, Hananiya, ta ƙaƙa Shaiɗan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya, ka kuma ɓoye wani abu daga kuɗin gonar? 4Kafin ka sayar, ba taka ba ce? Bayan ka sayar kuma, kuɗin ba halalinka ba ne? Ta ƙaƙa ka riya wannan aiki a zuciyarka? Ai, ba mutum ka yi wa ƙarya ba, Allah ka yi wa.” 5Da jin wannan magana Hananiya ya fāɗi ya mutu. Duk waɗanda suka ji kuwa, matsanancin tsoro ya kama su. 6Samari suka taso, suka sa shi a likkafani, suka ɗauke shi suka fitar da shi, suka je suka binne shi.
7Bayan misalin sa'a uku mata tasa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba. 8Sai Bitrus ya ce mata, “Gaya mini, shin, haka kuka sayar da gonar nan?” Sai ta ce, “I, haka ne.” 9Amma Bitrus ya ce mata, “Ƙaƙa kuka gama baki ku gwada Ruhun Ubangiji? Kin ji tafiyar waɗanda suka binne mijinki, har sun iso bakin ƙofa ma, za su kuwa ɗauke ki, su fitar da ke.” 10Nan tāke, ta fāɗi a gabansa, ta mutu. Da dai samarin suka shigo, suka iske ta matacciya, suka ɗauke ta suka fitar da ita, suka binne ta a jikin mijinta. 11Sai matsanancin tsoro ya kama dukan Ikkilisiyar, da kuma dukan waɗanda suka ji labarin waɗannan abubuwa.
An Yi Mu'ujizai da Abubuwan Al'ajabi Masu Yawa
12To, an yi mu'ujizai da abubuwan al'ajabi masu yawa a cikin mutane ta hannun manzanni. Dukansu kuwa da nufi ɗaya sukan taru a Shirayin Sulemanu. 13Amma a cikin sauran mutane ba wanda ya yi ƙarfin halin shiga cikinsu, duk da haka kuwa jama'a suna girmama su. 14Masu ba da gaskiya sai ƙaruwa suke ta yi ga Ubangiji fiye da dā, jama'a masu yawan gaske mata da maza. 15Har ma ya kai ga suna fito da marasa lafiya tafarku, suna shimfiɗa su a kan gadaje da tabarmi, don in Bitrus ya zo wucewa, ko da inuwa tasa ma ta bi ta kan waɗansunsu. 16Mutane kuwa suka yi ta taruwa daga garuruwan da suke kewayen Urushalima, suna ta kawo marasa lafiya da waɗanda baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, dukansu kuwa aka warkar da su.
An Tsananta wa Manzanni
17Amma babban firist ya taso, da duk waɗanda suke tare da shi, wato 'yan ɗariƙa Sadukiyawa, suna kishi gaya, 18suka kama manzannin, suka sa su kurkuku. 19Amma da daddare sai wani mala'ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun, ya fito da su, ya ce, 20“Ku tafi, ku tsaya a cikin Haikali, ku sanar da jama'a duk maganar wannan rai.” 21Da suka ji haka, suka shiga Haikalin da sassafe, suna koyarwa.
To, babban firist ya fito, shi da waɗanda suke tare da shi, suka kira majalisa, da dukan shugabannin Isra'ilawa, suka aika kurkuku a kawo su. 22Amma da dogaran Haikali suka je, ba su same su a kurkukun ba, suka dawo suka ba da labari, suka ce, 23“Mun iske kurkukun a kulle sosai, masu tsaro kuma na tsaro a bakin ƙofofin, amma da muka buɗe, sai muka tarar ba kowa a ciki.” 24To, da shugaban dogaran Haikali da manyan firistocin suka ji haka, suka ruɗe ƙwarai a game da su, suka rasa inda abin zai kai. 25Sai wani ya zo ya ce musu, “Ai, ga shi, mutanen nan da kuka sa a kurkuku suna nan a tsaye a Haikali, suna koya wa jama'a.” 26Sai shugaban dogaran Haikali da dogaran suka je suka kawo manzannin, amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada jama'a su jejjefe su da duwatsu.
27Da suka kawo su, suka tsai da su a gaban majalisar. Sai babban firist ya tambaye su, 28#Mat 27.25 ya ce, “Mun fa kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa da sunan nan, amma ga shi, kun gama Urushalima da koyarwarku, har ma kuna nema ku ɗafa mana alhakin jinin mutumin nan.” 29Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum. 30Allahn kakanninmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe ta wurin kafe shi a jikin gungume. 31Shi ne Allah ya ɗaukaka ga damansa, Shugaba da kuma Mai Ceto, domin ya buɗe wa Isra'ila hanyar tuba, su kuma sami gafarar zunubansu. 32Mu kuwa shaidu ne ga waɗannan al'amura, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya bai wa masu yi masa biyayya.”
33Da suka ji haka, sai suka husata ƙwarai da gaske, suna so su kashe su. 34Amma wani Bafarisiye, wai shi Gamaliyal, masanin Attaura, wanda duk jama'a suke girmamawa, ya miƙe cikin majalisa, ya yi umarni a fitar da mutanen nan waje tukuna. 35Sa'an nan ya ce musu, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku kula fa da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan. 36Shekarun baya wani mutum ya ɓullo, wai shi Tudas, yana mai da kansa wani abu, wajen mutum arbaminya kuma suka bi shi, amma aka kashe shi, mabiyansa kuwa aka watsa su, suka lalace. 37Bayansa kuma, a lokacin ƙirgen mutane, wai shi Yahuza Bagalile ya ɓullo, ya zuga waɗansu suka yi turu, suka bi shi. Shi ma ya hallaka, duk mabiyansa ma aka warwatsa su. 38To, yanzu ma, ina gaya muku, ku fita sha'anin mutanen nan, ku ƙyale su. Idan dai niyyarsu ko aikinsu na mutum ne, ai, zai rushe, 39amma in na Allah ne, ba dama ku rushe su. Kada fa a same ku kuna gāba da Allah.”
40Sai suka bi shawara tasa, suka kuma kirawo manzannin, suka yi musu dūka, suka kwaɓe su kada su ƙara magana da sunan Yesu, sa'an nan suka sake su. 41To, suka tashi daga gaban majalisar, suna farin ciki a kan an ga sun isa su sha wulakanci saboda sunan Yesu. 42Kowace rana kuwa, ko a Haikali ko a gida, ba su daina koyarwa da yin bishara, cewa Yesu shi ne Almasihu ba.
Currently Selected:
A.M 5: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979