Sai Bitrus ya ce, “Kai, Hananiya, ta ƙaƙa Shaiɗan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya, ka kuma ɓoye wani abu daga kuɗin gonar? Kafin ka sayar, ba taka ba ce? Bayan ka sayar kuma, kuɗin ba halalinka ba ne? Ta ƙaƙa ka riya wannan aiki a zuciyarka? Ai, ba mutum ka yi wa ƙarya ba, Allah ka yi wa.” Da jin wannan magana Hananiya ya fāɗi ya mutu. Duk waɗanda suka ji kuwa, matsanancin tsoro ya kama su.