A.M 7
7
Hanzarin Istifanas
1Sai babban firist ya ce, “Ashe, haka ne?” 2#Far 12.1 Sai Istifanas ya ce, “Ya ku 'yan'uwa da shugabanni, ku saurare ni. Allah Maɗaukaki ya bayyana ga kakanmu Ibrahim, sa'ad da yake ƙasar Bagadaza, tun bai zauna a Haran ba, 3ya ce masa, ‘Tashi daga ƙasarku, daga kuma cikin 'yan'uwanka, ka je ƙasar da zan nuna maka.’ 4#Far 11.31; Far 12.4 Sai ya tashi daga ƙasar Kaldiyawa, ya zauna a Haran. Daga can kuma, bayan mutuwar tsohonsa, Allah ya kawo shi ƙasar nan da yanzu kuke zaune. 5#Far 12.7; 13.15; 15.18; 17.8 Amma kuwa shi kansa, bai ba shi gādonta ba, ko da taki ɗaya, sai dai ya yi masa alkawari zai mallakar masa ita, shi da zuriyar bayansa, ko da yake ba shi da ɗa a lokacin. 6#Far 15.13,14 Abin da Allah ya faɗa kuwa shi ne zuriyar Ibrahim za su yi baƙunci a wata ƙasa, mutanen ƙasar kuwa za su bautar da su, su kuma gwada musu tasku har shekara arbaminya. 7#Fit 3.12 ‘Har wa yau kuma,’ Allah ya ce, ‘Al'ummar da za su bauta wa, ni zan hukunta ta, bayan haka kuma za su fito su bauta mini a wannan wuri.’ 8#Far 17.10-14; Far 21.2-4; Far 25.26; Far 29.31—35.18 Ya kuma yi masa alkawari game da kaciya. Ta haka, da Ibrahim ya haifi Ishaku, ya yi masa kaciya a rana ta takwas. Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi kakanninmu sha biyun nan.
9 #
Far 37.11;
Far 37.28;
Far 39.2,21 “Kakannin nan kuwa, da yake suna kishin Yusufu, suka sayar da shi, aka kai shi Masar. Amma Allah na tare da shi, 10#Far 41.39-41 ya kuma tsamo shi daga dukan wahala tasa, ya ba shi farin jini da hikima a gun Fir'auna, Sarkin Masar, shi kuwa ya naɗa shi mai mulkin Masar, ya kuma danƙa masa jama'ar gidansa duka. 11#Far 42.1,2 To, sai wata yunwa ta auku a dukan ƙasar Masar da ta Kan'ana, game da matsananciyar wahala, har kakanninmu suka rasa abinci. 12Amma da Yakubu ya ji akwai alkama a Masar, ya aiki kakanninmu tafiyar farko. 13#Far 45.1; Far 45.16 A tafiyarsu ta biyu Yusufu ya sanar da kansa ga 'yan'uwansa, asalinsa kuma ya sanu ga Fir'auna. 14#Far 45.9,10,17,18; Far 46.27 Sai Yusufu ya aika wa ubansa Yakubu yă zo, da kuma dukan 'yan'uwansa, mutum saba'in da biyar. 15#Far 46.1-7; Far 49.33 Sai Yakubu ya tafi Masar. A can ma ya mutu, shi da kakanninmu. 16#Far 23.3-16; 33.19; 50.7-13; Josh 24.32 Sai aka ɗebo su aka mai da su Shekem, aka sa su a kabarin da Ibrahim ya saya da kuɗi azurfa a wurin 'ya'yan Hamor a nan Shekem.
17 #
Fit 1.7,8 “Amma da lokacin cikar alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim ya gabato, jama'ar suka ƙaru, suka yawaita ƙwarai a ƙasar Masar, 18har aka yi wani sarki a Masar, wanda bai san ko wane ne Yusufu ba. 19#Fit 1.10,11; Fit 1.22 Wannan sarki kuwa ya cuci kabilarmu, yana gwada wa kakanninmu tasku, yana sawa a yar da jariransu, don kada su rayu. 20#Fit 2.2 A lokacin nan ne aka haifi Musa, yaro kyakkyawan gaske. Sai aka rene shi wata uku a gidan ubansa. 21#Fit 2.3-10 Da aka yar da shi waje, 'yar Fir'auna ta ɗauke shi tallafinta, ta goya shi kamar ɗanta. 22Sai aka karantar da Musa dukan ilimin Masarawa, shi kuwa mutum mai iko ne a cikin magana da ayyukansa.
23 #
Fit 2.11-15
“Yana gab da cika shekara arba'in ke nan, sai ya faɗo masa a rai yă ziyarci 'yan'uwansa Isra'ilawa. 24Da ya ga ana cutar ɗayansu, ya tare wanda ake wulakantawa, ya rama masa, ya buge Bamasaren, ya mutu. 25Ya zaci 'yan'uwansa sun gane ta hannunsa ne Allah zai cece su. Amma ba su gane ba. 26Kashegari kuma waɗansu suna faɗa, sai ya nemi shirya su, ya ce, ‘Ku jama'a, ku 'yan'uwa ne fa, don me kuke cutar juna?’ 27Amma mai cutar ɗan'uwa nasa ya ture Musa, ya ce, ‘Wa ya sa ka shugaba da alƙali a kanmu? 28Wato kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe Bamasaren nan na jiya?’ 29#Fit 18.3,4 Da jin wannan magana, Musa ya gudu ya yi baƙunci a ƙasar Madayana, inda ya haifi 'ya'ya biyu maza.
30 #
Fit 3.1-10
“To, bayan shekara arba'in, wani mala'ika ya bayyana a gare shi cikin harshen wuta, a wani kurmi a jejin Dutsen Sina'i. 31Da Musa ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya matso domin ya duba, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce, 32‘Ni ne Allahn kakanninka, Allahn Ibrahim da Ishaku da Yakubu.’ Sai jikin Musa ya ɗauki rawa, bai kuma iya ƙarfin halin dubawa ba. 33Sai Ubangiji ya ce masa, ‘Tuɓe takalminka, domin wurin da kake tsayen nan, tsattsarka wuri ne. 34Hakika, na ga wulakancin da ake yi wa mutanena da suke Masar, na ji nishinsu, na kuma sauko don in cece su. To, a yanzu sai ka zo in aike ka Masar.’
35 #
Fit 2.14
“To, shi Musan nan da suka ƙi, suna cewa, ‘Wa ya sa ka shugaba kuma alƙali?’ shi ne Allah ya aiko ya zama shugaba, da mai ceto, ta taimakon mala'ikan nan da ya bayyana a gare shi a cikin kurmin nan. 36#Fit 7.3; Fit 14.21; L.Ƙid 14.33 Shi ne kuwa ya fito da su, bayan ya yi abubuwan al'ajabi da mu'ujizai a ƙasar Masar, da Bahar Maliya, da kuma a cikin jeji, har shekara arba'in. 37#M.Sh 18.15,18 Wannan shi ne Musan da ya ce wa Isra'ilawa, ‘Allah zai tasar muku da wani annabi daga cikin 'yan'uwanku, kamar yadda ya tashe ni.’ 38#Fit 19.1—20.17; M.Sh 5.1-33 Shi ne kuma wanda yake a cikin Ikkilisiyar nan a jeji tare da mala'ikan da ya yi masa magana a Dutsen Sinai, tare da kakanninmu kuma. Shi ne kuma ya karɓo rayayyiyar magana domin ya kawo mana. 39Amma kakanninmu suka ƙi yi masa biyayya, suka ture shi, zuciya tasu ta koma ƙasar Masar. 40#Fit 32.1 Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana gumakan da za su yi mana jagaba, don Musan nan kam, da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya auku a gare shi ba.’ 41#Fit 32.2-6 A lokacin nan suka ƙera ɗan maraƙi, suka yanka wa gunkin nan hadaya, suka riƙa farin ciki da aikin da suka yi da hannunsu. 42#Amos 5.25-27 Saboda haka Allah ya juya musu baya, ya sallame su ga bautar taurari, yadda yake a rubuce a littafin annabawa cewa,
“ ‘Ya ku jama'ar Isra'ila,
Ni ne kuka yanka wa dabbobi, kuka miƙa wa hadaya,
Har shekara arba'in a cikin jeji?
43Ai, yawo kuka yi da alfarwar Molek,
Da surar tauraron gunki Ramfan,
Wato surorin nan da kuka ƙera don ku yi musu sujada.
Ni kuwa zan kawar da ku a can bayan Babila.’
44 #
Fit 25.9,40 “Dā kakanninmu suna da alfarwar shaida a jeji, irin wadda mai maganar nan da Musa ya umarta a yi, daidai fasalin da ya gani. 45#Josh 3.14-17 Alfarwan nan ita ce kakanninmu suka gāda, suka kuma kawo ƙasar nan a zamanin Joshuwa, bayan sun mallake ƙasar al'umman da Allah ya kora a gaban idonsu. Alfarwan nan kuwa tana nan har ya zuwa zamanin Dawuda, 46#2Sam 7.1-16; 1Tar 17.1-14 wanda ya sami tagomashi wurin Allah, har ya nemi alfarmar yi wa Allahn Yakubu masujada. 47#1Sar 6.1-38; 2Tar 3.1-17Amma Sulemanu ne ya yi wa Allah gini. 48Duk da haka Maɗaukaki ba ya zama a gidaje, ginin mutum. Yadda Annabi Ishaya ya ce,
49 #
Ish 66.1,2 “ ‘Allah ya ce, Sama ita ce kursiyina,
Ƙasa kuwa matashin ƙafata.
Wane wuri kuma za ku gina mini?
Ko kuwa wane wuri ne wurin hutuna?
50Ba da ikona na halicci dukan waɗannan abubuwa ba?’
51 #
Ish 63.10
“Ku kangararru, masu ɓatan basira, masu kunnen ƙashi, kullum kuna yi wa Ruhu Mai Tsarki tsayayya. Yadda kakanninku suka yi, haka ku ma kuke yi. 52A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa, 53ku ne kuwa kuka karɓi Shari'a ta wurin mala'iku, amma ba ku kiyaye ta ba!”
An Kashe Istifanas da Jifa
54Da suka ji haka, suka husata ƙwarai da gaske, har suka ciji baki don jin haushinsa. 55Amma Istifanas, a cike da Ruhu Mai Tsarki, sai ya zuba ido sama, ya ga ɗaukakar Allah, da kuma Yesu tsaye a dama ga Allah. 56Sai ya ce, “Ga shi, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗan Mutum tsaye dama ga Allah.” 57Amma suka ɗauki ihu ƙwarai, suka tattoshe kunnuwansu, suka aukar masa da nufi ɗaya, 58suka fitar da shi a bayan gari suka yi ta jifansa da dutse. Shaidu kuwa suka ajiye tufafinsu wurin wani saurayi, wai shi Shawulu. 59Suna ta jifan Istifanas, shi kuwa yana ta addu'a, yana cewa, “Ya Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” 60Sa'an nan ya durƙusa, ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Ya Ubangiji, kada ka ɗora musu wannan zunubi.” Da faɗar haka sai ya yi barci.
Currently Selected:
A.M 7: HAU
Highlight
Share
Copy
![None](/_next/image?url=https%3A%2F%2Fimageproxy.youversionapi.com%2F58%2Fhttps%3A%2F%2Fweb-assets.youversion.com%2Fapp-icons%2Fen.png&w=128&q=75)
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979