Far 8

8
Ƙarshen Ruwan Tsufana
1Allah kuwa ya tuna da Nuhu da dukan dabbobin gida da na jeji waɗanda suke cikin jirgi tare da shi. Allah ya sa iska ta hura bisa duniya, ruwaye suka janye. 2Maɓuɓɓugan zurfafa da tagogin sammai suka rufe, aka dakatar da ruwa daga sammai, 3ruwa ya yi ta janyewa daga duniya. Bayan kwana ɗari da hamsin sai ruwa ya ragu. 4Ya zama kuwa a ran sha bakwai ga wata na bakwai, sai jirgin ya tafi ya tsaya bisa kan dutsen Ararat. 5Ruwa ya yi ta raguwa har wata na goma. A ran ɗaya ga wata na goma, sai kawunan duwatsu suka ɓullo.
6A ƙarshen kwana arba'in Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, 7sai ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har lokacin da ruwan ya ƙafe a duniya. 8Sai kuma ya aiki kurciya ta gani ko ruwa ya janye, 9amma kurciyar ba ta sami inda za ta sauka ba, sai ta komo wurinsa cikin jirgi, gama har yanzu ruwa na rufe ƙasa duka. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauko ta ya shigar da ita cikin jirgi tare da shi. 10Ya jira kuma har kwana bakwai, sai kuma ya sāke aiken kurciyar daga cikin jirgin. 11Kurciyar kuwa ta komo wurinsa da maraice, ga shi kuwa, a bakinta sabon tohon zaitun wanda ta tsinko, domin haka Nuhu ya gane ruwa ya janye daga duniya. 12Sai ya sāke dakatawa har kwana bakwai, ya kuma aiki kurciya, amma ba ta ƙara komowa wurinsa ba.
13A rana ta fari ga wata na fari na shekara ta ɗari shida da ɗaya na Nuhu, ruwa ya ƙafe a duniya. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya duba, sai ga ƙasa busasshiya. 14Ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, duniya ta bushe.
15Sa'an nan sai Allah ya ce wa Nuhu, 16“Fito daga cikin jirgi, kai da matarka, da 'ya'yanka da matan 'ya'yanka tare da kai. 17Ka fito da kowane abu mai rai tare da kai, dukan talikai, wato tsuntsaye, da dabbobi, da kowane abu mai rarrafen da yake rarrafe bisa ƙasa, domin su hayayyafa su kuma riɓaɓɓanya a duniya.” 18Sai Nuhu ya fito, da 'ya'yansa, da matarsa da matan 'ya'yansa tare da shi, 19da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abin da yake motsi a bisa duniya, suka fito daga jirgi ɗaki ɗaki bisa ga irinsu.
Nuhu ya Miƙa Hadaya
20Nuhu ya gina wa Ubangiji bagade, ya ɗiba daga cikin kowace irin dabba mai tsarki, da kowane tsuntsu mai tsarki, ya miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden. 21Sa'ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, “Ba zan ƙara la'anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā. 22Muddin duniya tana nan, lokacin shuka da lokacin girbi, damuna da rani, yini da dare, ba za su daina ba.”

Pilihan Saat Ini:

Far 8: HAU

Sorotan

Berbagi

Salin

None

Ingin menyimpan sorotan di semua perangkat Anda? Daftar atau masuk