Far 7

7
Ruwan Tsufana
1Sai Ubangiji ya ce wa Nuhu, “Ka shiga jirgin, kai da iyalinka duka, gama na ga a wannan zamani, kai adali ne a gare ni. 2Daga cikin dabbobi masu tsarki ka ɗauki bakwai bakwai, namiji da ta mace, marasa tsarki kuwa namiji da ta mace, 3da kuma tsuntsayen sararin sama bakwai bakwai, namiji da ta mace, domin a wanzar da irinsu a duniya duka. 4Gama da sauran kwana bakwai kāna in sa a yi ruwa a duniya yini arba'in da dare arba'in. Dukan abu mai rai wanda na yi zan shafe shi daga duniya.” 5Nuhu kuwa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.
6Nuhu yana da shekara ɗari shida lokacin da Ruwan Tsufana ya kwararo bisa duniya. 7#Mat 24.38,39; Luk 17.27Nuhu da 'ya'yansa da matarsa, da matan 'ya'yansa tare da shi suka shiga jirgi, domin su tsira daga Ruwan Tsufana. 8Daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da na tsuntsaye, da na kowane mai rarrafe a ƙasa, 9biyu biyu, namiji da mata, suka shiga jirgi tare da Nuhu, kamar yadda Allah ya umarci Nuhu. 10Sai bayan kwana bakwai ruwayen suka kwararo bisa duniya.
11 # 2Bit 3.6 A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe. 12Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya yini arba'in da dare arba'in.
13A wannan rana Nuhu da 'ya'yansa, Shem, da Ham, da Yafet, da matar Nuhu da matan 'ya'yansa tare suka shiga jirgin, 14su da kowace dabbar jeji bisa ga irinta, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowane mai rarrafe wanda yake rarrafe bisa ƙasa, bisa ga irinsa, da kowane tsuntsun gida da na jeji wanda yake numfashi. 15-16Su waɗanda suka shiga, namiji ne da ta mace na kowane taliki, suka shiga jirgin kamar yadda Allah ya umarce shi. Sai Ubangiji ya kulle jirgi daga baya.
17Aka yi ta kwararo ruwa bisa duniya har kwana arba'in, ruwayen kuwa suka ƙaru, har suka ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can ƙoli birbishin duniya. 18Ruwa ya bunƙasa ya ƙaru ƙwarai bisa duniya, jirgin kuwa ya yi ta yawo bisa fuskar ruwaye. 19Ruwa kuwa ya bunƙasa ainun a bisa duniya, har ya rufe kawunan dukan duwatsu masu tsayi da yake ƙarƙashin sammai duka. 20Ruwa ya bunƙasa bisa duwatsu ya yi musu zara da ƙafa ashirin da biyar. 21Duk taliki wanda yake motsi bisa duniya ya mutu, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da na jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe bisa duniya, da kowane mutum, 22da kowane abin da yake bisa sandararriyar ƙasa wanda yake da numfashin rai cikin kafafen hancinsa ya mutu. 23Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi. 24Ruwa kuma ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.

Pilihan Saat Ini:

Far 7: HAU

Sorotan

Berbagi

Salin

None

Ingin menyimpan sorotan di semua perangkat Anda? Daftar atau masuk