Logo YouVersion
Îcone de recherche

Mat 22

22
Misali na Bikin Aure
1Yesu ya sāke yi musu magana da misalai ya ce, 2“Za a kwatanta Mulkin Sama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa biki. 3Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata bikin, amma waɗanda aka gayyatar suka ƙi zuwa. 4Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ’ 5Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gona tasa, wani kuma cinikinsa. 6Sauran kuwa suka kame bayinsa, suka wulaƙanta su, suka kashe su. 7Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus. 8Sa'an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin fa ya shiryu sosai, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba. 9Saboda haka ku tafi ƙofofin gari, ku gayyato duk waɗanda kuka samu, su zo bikin.’ 10Sai bayin suka yi ta bin titi titi, suka tattaro duk waɗanda suka samu, mugaye da nagargaru duka, har wurin bikin ya cika maƙil da baƙi.
11“Da sarki ya shigo ganin baƙin sai ya ga wani mutum a can wanda bai sa riga irin ta biki ba. 12Sai ya ce masa, ‘Malam, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba?’ Mutumin kuwa ya rasa ta cewa. 13#Mat 8.12; 25.30; Luk 13.28 Sai sarki ya ce wa barorinsa, ‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baƙi.’ 14Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”
Biyan Haraji ga Kaisar
(Mar 12.13-17; Luk 20.20-26)
15Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa. 16Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai. 17To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?” 18Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai! 19Ku nuna mini kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari. 20Yesu ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?” 21Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa'an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” 22Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.
Tambaya a kan Tashin Matattu
(Mar 12.18-27; Luk 20.27-40)
23 # A.M 23.8 A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya, 24#M.Sh 25.5 suka ce, “Malam, Musa dai ya ce, ‘In mutum ya mutu, bai bar na baya ba, sai lalle ɗan'uwansa ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.’ 25To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, da ya rasu, da yake bai haifu kuma ba, sai ya bar wa ɗan'uwansa matarsa. 26Haka ya faru ga na biyun da na ukun, har ya kai kan na bakwai ɗin. 27Bayansu duka sai matar ta rasu. 28To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu, su bakwai ɗin? Don duk sun aure ta.”
29Amma Yesu ya amsa musu ya ce, “Kun ɓăta ne, domin ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba. 30Domin a tashin matattu, ba a aure, ba a aurarwa, sai dai kamar mala'ikun da suke Sama ake. 31Game da tashin matattu, ashe, ba ku taɓa karanta abin da Allah ya ce muku ba? cewa, 32#Fit 3.6 ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.’ Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.” 33Da jama'a suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
Umarni Mafi Girma
(Mar 12.28-34; Luk 10.25-28)
34Amma da Farisiyawa suka ji ya ƙure Sadukiyawa, suka taru. 35Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Attaura, ya yi masa tambaya, yana gwada shi, ya ce, 36“Malam, wane umarni ne mafi girma a cikin Attaura?” 37#M.Sh 6.5 Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka. 38Wannan shi ne babban umarni na farko. 39#L.Fir 19.18 Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’ 40#Luk 10.25-28 A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.”
Tambaya a kan Ɗan Dawuda
(Mar 12.35-37; Luk 20.41-44)
41Tun Farisiyawa suna tare gu ɗaya, sai Yesu ya yi musu tambaya, 42ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.” 43Ya ce musu, “To, yaya kuwa Dawuda, ta ikon Ruhu, ya ce da shi Ubangiji? Har ya ce,
44 # Zab 110.1 “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
Zauna a damana,
Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’
45“Tun da Dawuda ya kira shi Ubangiji ne, to, ƙaƙa zai zama ɗansa?” 46Ba kuwa wanda ya iya tanka masa. Daga ran nan kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.

Sélection en cours:

Mat 22: HAU

Surbrillance

Partager

Copier

None

Tu souhaites voir tes moments forts enregistrés sur tous tes appareils? Inscris-toi ou connecte-toi