YouVersion Logo
Search Icon

Mika 4

4
Mulkin Salama na Ubangiji
(Ish 2.1-4)
1Zai zama nan gaba, dutse inda
Haikalin Ubangiji yake
Zai zama shi ne mafi tsawo duka a
cikin duwatsu,
Zai fi tuddai tsayi,
Mutane kuwa za su riƙa ɗunguma
zuwa wurinsa.
2Al'umman duniya za su zo, su ce,
“Bari mu haura zuwa tudun
Ubangiji,
Zuwa Haikalin Allah na Isra'ila,
Za mu koyi abin da yake so mu yi,
Za mu yi tafiya a hanyar da ya
zaɓa.”
Koyarwar Ubangiji daga Urushalima
take zuwa,
Daga Sihiyona yake magana da
jama'arsa.
3 # Ish 2.4; Yow 3.10 Zai shara'anta tsakanin al'umman
duniya masu yawa,
Zai sulhunta jayayyar da take tsakanin
manyan al'ummai,
Za su mai da takubansu garemani,
Māsunsu kuma su maishe su
wuƙaƙen aske itace.
Al'umma ba za ta ƙara fita zuwa
yaƙi ba,
Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.
4 # Zak 3.10 Kowa zai zauna gindin kurangar
inabinsa da gindin ɓaurensa.
Ba wanda zai tsoratar da shi,
Gama Ubangiji Mai Runduna ne ya
faɗa.
5Ko da yake al'ummai suna bin
gumakansu,
Amma mu za mu bi Ubangiji
Allahnmu har abada abadin.
Kuɓutar Isra'ila daga Zaman Talala
6Ubangiji ya ce,
“A waccan rana zan tattara guragu,
Da waɗanda aka kora,
Da waɗanda na wahalshe su.
7Zan sa guragu su wanzu,
Korarru kuwa su zama al'umma mai
ƙarfi,
Ni, Ubangiji, zan yi mulkinsu a
Sihiyona har abada.
8“Ke kuma hasumiyar garken tumaki,
tudun Sihiyona,
Mulki na dā zai komo wurinki,
Wato sarautar Urushalima.”
9Yanzu, me ya sa kike kuka da
ƙarfi?
Ba sarki a cikinki ne?
Mashawarcinki ya hallaka ne,
Da azaba ta auka miki kamar ta
mace mai naƙuda?
10Ki yi makyarkyata, ki yi nishi, ke
Sihiyona,
Kamar mace mai naƙuda,
Gama yanzu za ki fita daga cikin
birni,
Ki zauna a karkara,
Za ki tafi Babila, daga can za a cece
ki.
Daga can Ubangiji zai cece ki daga
hannun maƙiyanki.
11Yanzu al'ummai sun taru suna
gāba da ke, suna cewa,
“Bari a ƙazantar da ita,
Bari mu zura mata ido.”
12Amma ba su san nufin Ubangiji ba,
Ba su gane shirinsa ba,
Gama ya tara su ne kamar
dammunan da za a kai
masussuka.
13“Ya Sihiyona, ki tashi, ki tattaka!
Gama zan mai da ƙahonki ƙarfe,
kofatanki kuwa tagulla,
Za ki ragargaje al'ummai da yawa.”
Za ki ba Ubangijin dukan duniya
dukiyarsu da suka tara ta hanyar
zamba,
Wadatarsu kuma ga Ubangijin dukan
duniya.

Currently Selected:

Mika 4: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in