Al'umman duniya za su zo, su ce,
“Bari mu haura zuwa tudun
Ubangiji,
Zuwa Haikalin Allah na Isra'ila,
Za mu koyi abin da yake so mu yi,
Za mu yi tafiya a hanyar da ya
zaɓa.”
Koyarwar Ubangiji daga Urushalima
take zuwa,
Daga Sihiyona yake magana da
jama'arsa.