YouVersion Logo
Search Icon

Mika 3

3
An Yi wa Shugabannin Isra'ila Faɗa
1Ni kuwa na ce, “Ku ji, ya ku
shugabannin mutanen Yakubu,
Da ku sarakunan Isra'ila.
Ya kamata ku san shari'a.
2Amma kuna ƙin nagarta, kuna
ƙaunar mugunta,
Kuna feɗe mutanena,
Kuna kuma fizge naman jikinsu daga
ƙasusuwansu.
3Kuna cin naman mutanena, kuna
feɗe fatar jikinsu,
Kuna kakkarya ƙasusuwansu,
Kuna yanyanka su gunduwa
gunduwa kamar naman da za a sa
a tukunya.”
4Sa'an nan za su yi kuka ga Ubangiji,
Amma Ubangiji ba zai amsa musu
ba.
Zai ɓoye musu fuskarsa a wannan
lokaci,
Saboda mugayen ayyukansu.
5Ga abin da Ubangiji ya ce a kan
annabawan da suka bi da
mutanensa a karkace,
Waɗanda suke cewa, “Salama,”
sa'ad da suke da abinci,
Amma sukan kai yaƙin shahada
Ga wanda bai ba su abin sawa a baka
ba.
6Saboda haka kome zai zama dare
da duhu, ba wahayi ko duba.
Rana za ta fāɗi a kan annabawa,
Yini zai zama musu duhu baƙi
ƙirin.
7Masu gani za su sha kunya,
Masu duba kuwa za su ruɗe,
Dukansu za su rufe bakinsu,
Gama ba amsa daga wurin Allah.
8Amma ni ina cike da iko,
Da Ruhun Ubangiji,
Da shari'a da ƙarfin hali,
Don in sanar wa Yakubu da laifinsa,
Isra'ila kuma da zunubinsa.
9Ku ji wannan, ya ku shugabannin
jama'ar Yakubu,
Da ku sarakunan mutanen Isra'ila,
Ku da kuke ƙyamar shari'ar gaskiya,
Kuna karkatar da dukan gaskiya.
10Kuna gina Sihiyona da jini,
Kuna kuwa gina Urushalima da
zalunci.
11Shari'ar shugabannin ƙasar ta cin
hanci ce.
Firistocinta suna koyarwa don
neman riba,
Haka kuma annabawa suna annabci
don neman kuɗi.
Duk da haka suna dogara ga
Ubangiji, suna cewa,
“Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu,
Ba masifar da za ta same mu.”
12 # Irm 26.18 Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona
kamar gona,
Urushalima kuwa za ta zama tsibin
kufai,
Dutse inda Haikali yake zai zama
kurmi.

Currently Selected:

Mika 3: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in