YouVersion Logo
Search Icon

Mat 4

4
Shaiɗan Ya Gwada Yesu
(Mar 1.12-13; Luk 4.1-13)
1 # Ibr 2.18; 4.15 Sa'an nan sai Ruhu ya kai Yesu cikin jeji, domin Iblis yă gwada shi. 2Da ya yi azumi kwana arba'in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi. 3Sai Mai Gwadawar nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.” 4#M.Sh 8.3 Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,
“ ‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba,
Sai dai da kowace maganar da yake fitowa daga wurin Allah.’ ”
5Sa'an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, 6#Zab 91.11,12 ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to dira ƙasa. Don a rubuce yake cewa,
‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai,’
da kuma
‘Za su tallafe ka,
Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”
7 # M.Sh 6.16 Sai Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ” 8Har wa yau dai, sai Iblis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo ƙwarai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu. 9Ya kuma ce masa, “Duk waɗannan zan ba ka in ka faɗi a gabana ka yi mini sujada.” 10#M.Sh 6.13 Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa,
‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada,
Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”
11Sa'an nan Iblis ya rabu da shi. Sai ga mala'iku sun zo suna yi masa hidima.
Yesu Ya Fara Hidima a Galili
(Mar 1.14-15; Luk 4.14-15)
12 # Mat 14.3; Mar 6.17; Luk 3.19,20 To, da Yesu ya ji an tsare Yahaya, sai ya tashi zuwa ƙasar Galili. 13#Yah 2.12 Ya kuma bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin teku, a kan iyakar ƙasar Zabaluna da Naftali, 14domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,
15 # Ish 9.1,2 “Ƙasar Zabaluna da ƙasar Naftali,
Da bakin bahar, da hayin Kogin Urdun,
Da kuma ƙasar Galili ta al'ummai,
16Mazaunan duhu sun ga babban haske,
Mazaunan bakin mutuwa da fargabarta,
Haske ya keto musu.”
17 # Mat 3.2 Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.”
Yesu Ya Kira Masunta Huɗu
(Mar 1.16-20; Luk 5.1-11)
18Yana tafiya a bakin Tekun Galili ke nan, sai ya ga waɗansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, don su masunta ne. 19Sai ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.” 20Nan da nan, sai suka watsar da tarunansu, suka bi shi. 21Da ya ci gaba sai ya ga waɗansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da ubansu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su. 22Nan take suka bar jirgin duk da ubansu, suka bi shi.
Yesu Ya Hidimanta wa Mutane Masu Yawa
(Luk 6.17-19)
23 # Mat 9.35; Mar 1.39 Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane. 24Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su. 25Taro masu yawan gaske suka bi shi daga ƙasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da ƙasar Yahudiya, har ma daga hayin Kogin Urdun.

Currently Selected:

Mat 4: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in