YouVersion Logo
Search Icon

Mat 5

5
Wa'azi a kan Dutse
(Mat 5.1—7.29)
1Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Da ya zauna, almajiransa kuma suka zo gunsa. 2Sai ya buɗe baki ya koya musu.
Albarku
(Luk 6.20-23)
3“Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.
4 # Ish 61.2 “Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.
5 # Zab 37.11 “Albarka tā tabbata ga masu tawali'u, domin za su gāji duniya.
6 # Ish 55.1,2 “Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.
7“Albarka tā tabbata ga majiya tausayi, domin su ma za a ji tausayinsu.
8 # Zab 24.3,4 “Albarka tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, domin za su ga Allah.
9“Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su 'ya'yan Allah.
10 # 1Bit 3.14 “Albarka tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata adalci, domin Mulkin Sama nasu ne.
11 # 1Bit 4.14 “Albarka tā tabbata gare ku sa'ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni. 12#2Tar 36.16; A.M 7.52 Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku.”
Gishiri da Haske
(Mar 9.50; Luk 14.34-35)
13 # Mar 9.50; Luk 14.34,35 “Ku ne gishirin duniya. Amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar, mutane kuma su tattake.
14 # Yah 8.12; 9.5 “Ku ne hasken duniya. Ai, birnin da aka gina bisa tudu ba shi ɓoyuwa. 15#Mar 4.21; Luk 8.16; 11.33 Ba a kunna fitila a rufe ta da masaki, sai dai a ɗora ta a kan maɗorinta, sa'an nan ta ba duk mutanen gida haske. 16#1Bit 2.12 To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, domin su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da yake cikin Sama.”
Koyarwar Yesu a kan Attaura
17“Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zo ne ba domin in shafe su ba, sai dai domin in cika su. 18#Luk 16.17 Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome. 19Don haka duk wanda ya yar da umarni ɗaya mafi ƙanƙanta daga cikin umarnan nan, har ya koya wa mutane haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a Mulkin Sama. Duk wanda ya bi su kuwa, har ya koyar da su, za a ce da shi mai girma a Mulkin Sama. 20Ina dai gaya muku, in adalcinku bai fi na malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.”
Koyarwar Yesu a kan Fushi
(Luk 12.57-59)
21 # Fit 20.13; M.Sh 5.17 “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.’ 22Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta. 23Saboda haka, in kana cikin miƙa sadakarka a kan bagadin hadaya, a nan kuma ka tuna ɗan'uwanka na da wata magana game da kai, 24sai ka dakatar da sadakarka a gaban bagadin hadaya tukuna, ka je ku shirya da ɗan'uwanka, sa'an nan ka zo ka miƙa sadakarka. 25Ka hanzarta shiryawa da mai ƙararka tun kuna tafiya gaban shari'a, don kada mai kararka ya bashe ka ga alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga dogari, a kuma jefa ka a kurkuku. 26Hakika ina gaya maka, ba za ka fita daga nan ba, sai ka biya duk, babu sauran ko anini.”
Koyarwar Yesu a kan Zina
27 # Fit 20.14; M.Sh 5.18 “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ 28Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha'awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita. 29#Mat 18.9; Mar 9.47 In idonka na dama yana sa ka yi laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa duk jikinka ɗungum a Gidan Wuta. 30#Mat 18.8; Mar 9.43In kuma hannunka na dama, yana sa ka yi laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa jikinka ɗungum a Gidan Wuta.”
Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure
(Mat 19.9; Mar 10.11-12; Luk 16.18)
31 # M.Sh 24.1-4; Mat 19.7; Mar 10.4 “An kuma ce, ‘Kowa ya saki matarsa, sai ya ba ta takardar saki.’ 32#Mat 19.9; Mar 10.11,12; Luk 16.18; 1Kor 7.10,11 Amma ni ina gaya muku, kowa ya saki matarsa, in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta hanyar zina ke nan. Wanda kuma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”
Koyarwar Yesu a kan Rantsuwa
33 # L.Fir 19.12; L.Ƙid 30.2; M.Sh 23.21 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka rantse a kan ƙarya, sai dai ka cika wa'adin da ka ɗaukar wa Ubangiji.’ 34#Yak 5.12; Ish 66.1; Mat 23.22 Amma ni ina gaya muku, kada ma ku rantse sam, ko da sama, domin ita ce kursiyin Allah, 35#Ish 66.1; Zab 48.2 ko da ƙasa, domin ita ce matashin ƙafarsa, ko kuma da Urushalima, domin ita ce birnin Babban Sarki. 36Kada kuwa ka rantse da kanka, don ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya fari ko baƙi ba. 37Abin da duk za ku faɗa ya tsaya a kan ‘I’ ko ‘A'a’ kawai. In dai ya zarce haka, to, daga Mugun ya fito.”
Koyarwar Yesu a kan Ramawa
(Luk 6.29-30)
38 # Fit 21.24; L.Fir 24.20; M.Sh 19.21 “Kun dai ji an faɗa, ‘Sakayyar ido, ido ne, sakayyar haƙori kuma haƙori ne.’ 39Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma. 40In kuwa wani ya yi ƙararka da niyyar karɓe taguwarka, to, ka bar masa mayafinka ma. 41In kuma wani ya tilasta maka ku yi tafiyar mil guda tare, to, ku yi tafiyar mil biyu ma. 42Kowa ya roƙe ka, ka ba shi, mai neman rance a wurinka kuwa, kada ka hana shi.”
Ƙaunar Magabta
(Luk 6.27-28,32-36)
43“Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan'uwanka, ka ƙi magabcinka.’ 44Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu'a, 45domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci. 46In masoyanku kawai kuke ƙauna, wane lada ne da ku? Ashe, ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47In kuwa 'yan'uwanku kaɗai kuke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe, ko al'ummai ma ba haka suke yi ba? 48#L.Fir 19.2; M.Sh 18.13 Saboda haka sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na Sama take cikakke.”

Currently Selected:

Mat 5: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in