Farawa 6

6
Mugunta a duniya
1Sa’ad da mutane suka fara ƙaruwa a duniya, aka kuma hahhaifi musu ’ya’ya mata, 2sai ’ya’yan Allah maza suka ga cewa ’ya’yan mutane mata suna da bansha’awa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura. 3Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.”
4Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da ’ya’yan Allah suka kwana da ’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara.
5 Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci. 6Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai. 7Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.” 8Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.
9Ga tarihin Nuhu.
Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah. 10Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.
11Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali. 12Allah ya ga yadda duniya ta lalace, gama dukan mutane a duniya sun lalatar da rayuwarsu. 13Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya. 14Saboda haka ka yi wa kanka jirgi da katakon Saifires#6.14 Babu tabbas game da ma’anar kalman nan a Ibraniyanci., ka yi ɗakuna a cikinsa, ka shafe shi da ƙaro ciki da waje. 15Ga yadda za ka gina shi; jirgin zai kasance mai tsawon ƙafa 45, fāɗinsa ƙafa 75, tsayinsa kuma ƙafa 45. 16Ka yi masa rufi, ka kuma ba da fili inci 18 tsakanin rufin a kowane gefen jirgin.#6.16 Ko kuwa Ka bar inda haske zai shiga ta wurin gamawa Ka sa ƙofa a gefen jirgin. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe. 17Ga shi zan aiko da ambaliya ruwa a duniya, in hallaka dukan mai rai da yake a ƙarƙashin sama, kowace halittar da take numfashi a cikinta. Dukan abin da yake a duniya zai hallaka. 18Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da ’ya’yanka maza da matarka da matan ’ya’yanka tare da kai. 19Za ka shigar da biyu na dukan halittu masu rai, namiji da ta mace a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai. 20Biyu na kowane irin tsuntsu, kowace irin dabba da kuma kowace irin halitta mai rarrafe a ƙasa, za su zo wurinka domin a bar su da rai. 21Za ka ɗauki kowane irin abinci wanda za a ci, ka adana don yă zama abincinka da nasu.”
22Nuhu ya yi kome kamar yadda Allah ya umarce shi.

Àwon tá yàn lọ́wọ́lọ́wọ́ báyìí:

Farawa 6: SRK

Ìsàmì-sí

Pín

Daako

None

Ṣé o fẹ́ fi àwọn ohun pàtàkì pamọ́ sórí gbogbo àwọn ẹ̀rọ rẹ? Wọlé pẹ̀lú àkántì tuntun tàbí wọlé pẹ̀lú àkántì tí tẹ́lẹ̀