Allah ya ba ka daga cikin raɓar
sama,
Daga cikin ni'imar ƙasa,
Da hatsi a yalwace da ruwan inabi.
Bari jama'a su bauta maka,
Al'ummai kuma su sunkuya maka.
Za ka yi shugabancin 'yan'uwanka,
Allah ya sa 'ya'yan mahaifiyarka su
sunkuya maka.
La'ananne ne dukan wanda ya
la'anta ka,
Albarkatacce ne dukan wanda ya sa
maka albarka.”