Yah 15
15
Yesu Ne Itacen Inabi na Hakika
1“Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi. 2Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa. 3Koyanzu ma ku tsarkakku ne saboda maganar da na faɗa muku. 4Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya 'ya'ya shi kaɗai, sai ko ya zauna itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina. 5Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin 'ya'ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba. 6Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone. 7In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku. 8Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna 'ya'ya da yawa, ta haka kuma kuke tabbata almajiraina. 9Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, ku zauna cikin ƙaunar da nake muku. 10In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini. 11Na gaya muku haka domin farin cikina ya kasance a cikinku, farin cikinku kuma ya zama cikakke.
12 #
Yah 13.34; 15.17; 1Yah 3.23; 2Yah 1.5 “Wannan fa shi ne umarnina, cewa ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum yă ba da ransa saboda aminansa. 14Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku. 15Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana. 16Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku. 17Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.”
Ƙiyayyar Duniya
18In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku. 19Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20#Mat 10.24; Luk 6.40; Yah 13.16 Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, “Bawa ba ya fin ubangijinsa.” In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma. 21Duk wannan za su yi muku saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba. 22Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu. 23Wanda ya ƙi ni ya ƙi Ubana ma. 24Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka. 25#Zab 35.19; 69.4 An yi wannan kuwa domin a cika maganar da yake a rubuce a cikin Shari'arsu cewa, “Sun ƙi ni ba dalili.” 26Amma sa'ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaida ni. 27Ku ma shaidu ne, domin tun farko kuke tare da ni.
ಪ್ರಸ್ತುತ ಆಯ್ಕೆ ಮಾಡಲಾಗಿದೆ:
Yah 15: HAU
Highlight
ಶೇರ್
ಕಾಪಿ
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979