1
Yah 15:5
Littafi Mai Tsarki
Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin 'ya'ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba.
Compare
Explore Yah 15:5
2
Yah 15:4
Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya 'ya'ya shi kaɗai, sai ko ya zauna itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina.
Explore Yah 15:4
3
Yah 15:7
In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku.
Explore Yah 15:7
4
Yah 15:16
Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku.
Explore Yah 15:16
5
Yah 15:13
Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum yă ba da ransa saboda aminansa.
Explore Yah 15:13
6
Yah 15:2
Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa.
Explore Yah 15:2
7
Yah 15:12
“Wannan fa shi ne umarnina, cewa ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.
Explore Yah 15:12
8
Yah 15:8
Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna 'ya'ya da yawa, ta haka kuma kuke tabbata almajiraina.
Explore Yah 15:8
9
Yah 15:1
“Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi.
Explore Yah 15:1
10
Yah 15:6
Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone.
Explore Yah 15:6
11
Yah 15:11
Na gaya muku haka domin farin cikina ya kasance a cikinku, farin cikinku kuma ya zama cikakke.
Explore Yah 15:11
12
Yah 15:10
In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini.
Explore Yah 15:10
13
Yah 15:17
Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.”
Explore Yah 15:17
14
Yah 15:19
Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.
Explore Yah 15:19
ಮುಖಪುಟ
ಬೈಬಲ್
ಯೋಜನೆಗಳು
ವೀಡಿಯೊಗಳು