Mat 27

27
Yesu a Gaban Bilatus
(Mar 15.1; Luk 23.1-2; Yah 18.28-32)
1Da gari ya waye sai duk manyan firistoci da shugabannin jama'a suka yi shawara a kan Yesu su kashe shi. 2Sai suka ɗaure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga mai mulki Bilatus.
Mutuwar Yahuza
(A.M 1.18-20)
3 # A.M 1.18,19 Sa'ad da Yahuza mai bashe shi ya ga an yanke masa hukuncin kisa, sai ya yi nadama, ya mayar wa manyan firistoci da shugabanni da kuɗi azurfa talatin ɗin nan, 4ya ce, “Na yi zunubi da na ba da marar laifi a kashe shi.” Suka ce, “Ina ruwanmu? Kai ka jiyo!” 5Sai ya watsar da kuɗin azurfan nan a Haikali, ya fita, ya je ya rataye kansa. 6Amma manyan firistoci suka tsince kuɗin suka ce, “Bai halatta mu zuba su a Baitulmalin Haikali ba, don kuɗin ladan kisankai ne.” 7Sai suka yi shawara, suka sayi filin maginin tukwane da kuɗin don makabartar baƙi. 8Don haka, har ya zuwa yau, ana kiran filin nan filin jini. 9#Zak 11.12,13 Ta haka aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa, “Sun ɗauki kuɗin azurfa talatin ɗin nan, wato, awalajar shi wannan da waɗansu Isra'ilawa suka yi wa kima, 10suka sayi filin maginin tukwane da su, yadda Ubangiji ya umurce ni.”
Bilatus Ya Tuhumi Yesu
(Mar 15.2-5; Luk 23.3-5; Yah 18.33-38)
11To, sai Yesu ya tsaya a gaban mai mulki, mai mulkin kuma ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa.” 12Amma da manyan firistoci da shugabanni suka kai ƙararrakinsa, bai ce kome ba. 13Sai Bilatus ya ce masa, “Ba ka ji yawan maganganun da suke ba da shaida a kanka ba?” 14Amma bai ba shi wata amsa, ko da ta kalma ɗaya ba, har mai mulki ya yi mamaki ƙwarai.
An Hukunta wa Yesu Mutuwa
(Mar 15.6-15; Luk 23.13-25; Yah 18.39—19.16)
15To, a lokacin idi kuwa mai mulki ya saba sakar wa jama'a kowane ɗaurarre guda da suka so. 16A lokacin kuwa da wani shahararren ɗan sarƙa, mai suna Barabbas. 17Da suka taru sai Bilatus ya ce musu, “Wa kuke so in sakar muku? Barabbas ko kuwa Yesu da ake kira Almasihu?” 18Don ya sani saboda hassada ne suka bashe shi. 19Banda haka kuma, a lokacin da yake zaune a kan gadon shari'a, sai mata tasa ta aiko masa da cewa, “Ka fita daga sha'anin mara laifin nan, don yau na sha wahala ƙwarai a mafarkinsa.” 20To, sai manyan firistoci da shugabanni suka rarrashi jama'a su zaɓi Barabbas, Yesu kuwa a kashe shi. 21Sai mai mulki ya sāke ce musu, “Wane ne a cikin biyun nan kuke so in sakar muku?” Sai suka ce, “Barabbas.” 22Bilatus ya ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da Yesu da ake kira Almasihu?” Duk sai suka ce, “A gicciye shi!” 23Ya ce, “Ta wane halin? Wane mugun abu ya yi?” Amma su sai ƙara ɗaga murya suke ta yi, suna cewa, “A gicciye shi!”
24 # M.Sh 21.6-9 Da Bilatus ya ga bai rinjaye su ba, sai dai hargitsi yana shirin tashi, sai ya ɗibi ruwa ya wanke hannunsa a gaban jama'a, ya ce, “Ni kam, na kuɓuta daga alhakin jinin mai adalcin nan. Wannan ruwanku ne.” 25Sai duk jama'a suka amsa suka ce, “Alhakin jininsa a wuyanmu, mu da 'ya'yanmu!” 26Sa'an nan ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi a gicciye shi.
Sojoji Sun Yi wa Yesu Ba'a
(Mar 15.16-20; Yah 19.2-3)
27Sai sojan mai mulki suka kai Yesu cikin fadar mai mulki, suka tara dukan ƙungiyar soja a kansa. 28Sai suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar alkyabba. 29Suka yi wani rawani na ƙaya, suka sa masa a kā, suka danƙa masa sanda a hannunsa na dama, suka kuma durƙusa a gabansa, suna yi masa ba'a suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” 30Suka tattofa masa yau, suka karɓe sandan, suka ƙwala masa a ka. 31Da suka gama yi masa ba'a, sai suka yaye masa alkyabbar, suka sa masa nasa tufafi, suka tafi da shi su gicciye shi.
An Gicciye Yesu
(Mar 15.21-32; Luk 23.26-43; Yah 19.17-27)
32Suna tafiya ke nan, sai suka gamu da wani Bakurane, mai suna Saminu. Shi ne suka tilasta wa ya ɗauki gicciyen Yesu.
33Da suka isa wurin da ake kira Golgota, wato, wurin ƙoƙwan kai, 34#Zab 69.21 suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha, amma da ya ɗanɗana sai ya ƙi sha. 35#Zab 22.18 Da suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu ta jefa kuri'a. 36Suka zauna a nan suna tsaronsa. 37A daidai kansa aka kafa sanarwar laifinsa cewa, “Wannan shi ne Yesu, Sarkin Yahudawa.” 38Sai kuma aka gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a dama, ɗaya a hagun. 39#Zab 22.7; 109.25 Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai, 40#Mat 26.61; Yah 2.19 suna cewa, “Kai da za ka rushe Haikalin, ka kuma gina shi a cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, to sauko daga gicciyen mana!” 41Haka kuma manyan firistoci da malaman Attaura da shugabanni suka riƙa yi masa ba'a, suna cewa, 42“Ya ceci waɗansu, ya kuwa kasa ceton kansa. Ai, Sarkin Isra'ila ne, yă sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mā gaskata da shi. 43#Zab 22.8 Yā dogara ga Allah, to, Allah ya cece shi mana yanzu, in dai yana sonsa, don ya ce wai shi Ɗan Allah ne.” 44Har 'yan fashin nan da aka gicciye su tare ma, su suka zazzage shi kamar waɗancan.
Mutuwar Yesu
(Mar 15.33-41; Luk 23.44-49; Yah 19.28-30)
45To, tun daga tsakar rana, duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma. 46#Zab 22.1 Wajen ƙarfe uku kuma sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāni?” Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” 47Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, sai suka ce, “Mutumin nan na kiran Iliya ne.” 48#Zab 69.21 Sai nan da nan ɗaya daga cikinsu ya yiwo gudu, ya ɗauko soso ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha. 49Amma sauran suka ce, “Ku bari mu gani ko Iliya zai zo ya ceci shi.” 50Sai Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sa'an nan ya săki ransa.
51 # Fit 26.31-33 Sai labulen da yake cikin Haikalin ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta yi girgiza, duwatsu kuma suka tsattsage. 52Aka bubbuɗe kaburbura, tsarkaka da yawa da suke barci kuma suka tashi. 53Suka firfito daga kaburburan, bayan ya tashi daga matattu, sai suka shiga tsattsarkan birnin, suka bayyana ga mutane da yawa. 54Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”
55 # Luk 8.2,3 Akwai kuma waɗansu mata da yawa a can suna hange daga nesa, waɗanda suka biyo Yesu tun daga ƙasar Galili, suna yi masa hidima. 56A cikinsu da Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu da Yusufu, da kuma uwar 'ya'yan Zabadi.
Jana'izar Yesu
(Mar 15.42-47; Luk 23.50-56; Yah 19.38-42)
57Maraice lis sai wani mai arziki ya zo, mutumin Arimatiya, mai suna Yusufu, shi ma almajirin Yesu ne. 58Ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya yi umarni a ba shi. 59Yusufu ya ɗauki jikin, ya sa shi a likkafanin lilin mai tsabta, 60ya sa shi a wani sabon kabari da ya tanadar wa kansa, wanda ya fafe a jikin dutse. Sai ya mirgina wani babban dutse a bakin kabarin, ya tafi. 61Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun suna nan zaune a gaban kabarin.
Masu Tsaron Kabarin
62Kashegari, wato, bayan ranar shiri, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka taru a gaban Bilatus, 63#Mat 16.21; 17.23; 20.19; Mar 8.31; 9.31; 10.33,34; Luk 9.22; 18.31-33 suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu. 64Saboda haka sai ka yi umarni a tsare kabarin nan sosai har rana ta uku, kada almajiransa su sace shi, sa'an nan su ce wa mutane wai ya tashi daga matattu. Yaudarar ƙarshe za ta fi ta farkon muni ke nan.” 65Sai Bilatus ya ce musu, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare shi iyakar ƙoƙarinku.” 66Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka buga wa dutsen nan hatimi, suka kuma sa sojan tsaro.

Currently Selected:

Mat 27: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in