1
Mat 27:46
Littafi Mai Tsarki
Wajen ƙarfe uku kuma sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāni?” Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”
Compare
Explore Mat 27:46
2
Mat 27:51-52
Sai labulen da yake cikin Haikalin ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta yi girgiza, duwatsu kuma suka tsattsage. Aka bubbuɗe kaburbura, tsarkaka da yawa da suke barci kuma suka tashi.
Explore Mat 27:51-52
3
Mat 27:50
Sai Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sa'an nan ya săki ransa.
Explore Mat 27:50
4
Mat 27:54
Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”
Explore Mat 27:54
5
Mat 27:45
To, tun daga tsakar rana, duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.
Explore Mat 27:45
6
Mat 27:22-23
Bilatus ya ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da Yesu da ake kira Almasihu?” Duk sai suka ce, “A gicciye shi!” Ya ce, “Ta wane halin? Wane mugun abu ya yi?” Amma su sai ƙara ɗaga murya suke ta yi, suna cewa, “A gicciye shi!”
Explore Mat 27:22-23
Home
Bible
გეგმები
ვიდეოები