Luka Gabatarwa
Gabatarwa
Gabatarwa
Luka ne marubucin wannan bishara. Shi likita ne kuma ba mutumin Yahuda ba ne. Shi ba ɗaya ba ne cikin almajiran Yesu kamar sauran marubutan Littattafan Bisharar Yesu, ko da yake akwai alama ya sadu da waɗansu daga cikin almajiran Yesu (1.2). Ana zato an rubuta bisharan nan tsakanin shekara ta 59 da shekara ta 63 bhy, ko kuwa shekara ta 70 zuwa 80 bhy. An rubuta littattafan Luka da Ayyukan Manzanni a matsayin tarihi ne. Littafin Luka labarin rayuwa, aiki, mutuwa, da tashi daga mutuwar Yesu ne. Littafin Ayyukan Manzanni ne ya cika wannan. Wannan ya nuna yadda almajiran Yesu suka yaɗa labari mai daɗi na Yesu Kiristi a dukan fāɗin masarautar Roma a karni na fari. An yi rubutun a hanya da kuma salo na yadda marubutan tarihi suka bi na rubutu, wannan Bishara ta nuna aikin Yesu a matsayin cikar alkawarin Allah da kuma ƙaunar ceto ga mutanensa. Littafin ya cika da bayyanannen tarihi. Ya kuma ƙunshi labaru masu yawa game da Yesu, haɗe da misalan (labaru) da Yesu ya koyar da ba sa a cikin sauran Bisharu. Masana sun nuna cewa Luka “ya yi hange mai nisa,” yana nuna yadda abubuwa da kuma lokacin aikin Yesu sun dace daidai da shirin Allah don halittarsa.
Pilihan Saat Ini:
Luka Gabatarwa: SRK
Sorotan
Berbagi
Salin

Ingin menyimpan sorotan di semua perangkat Anda? Daftar atau masuk
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.