Luka 19
19
Zakka mai karɓar haraji
1Yesu ya shiga Yeriko, yana ratsa ta cikinta. 2Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma. 3Ya so yă ga ko wane ne Yesu, amma saboda taron, bai iya ba, domin shi gajere ne. 4Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don yă gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne.
5Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.” 6Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna.
7Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, “Ya je don yă zama baƙon ‘mai zunubi.’ ”
8Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.”
9Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne. 10Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”
Misalin mina goma
(Mattiyu 25.14-30)
11Yayinda suna cikin sauraron wannan, sai ya ci gaba da gaya musu wani misali, domin ya yi kusa da Urushalima, kuma mutanen suna tsammani mulkin Allah zai bayyana, nan da nan. 12Ya ce, “Wani mutum mai martaba ya tafi wata ƙasa mai nisa don a naɗa shi sarki sa’an nan ya dawo. 13Saboda haka ya kira bayinsa goma ya ba su mina goma. Ya ce, ‘Ku yi kasuwanci da kuɗin nan, sai na dawo.’
14 “Amma talakawansa suka ƙi shi, sai suka aikar da wakilai bayansa, domin su ce, ‘Ba mu son wannan mutum ya zama sarkinmu.’
15 “Duk da haka, aka naɗa shi sarki, sa’an nan ya dawo gida. Sai ya aika aka kira bayin da ya ba su kuɗin, don yă san ribar da suka samu.
16 “Na fari ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar goma.’
17 “Maigidan ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawana mai kirki! Tun da ka yi aminci a kan abu ƙanƙani, ka yi riƙon birane goma.’
18 “Na biyun ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar biyar.’
19 “Maigidansa ya ce, ‘Kai ka yi riƙon birane biyar.’
20 “Sai wani bawan ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ga minarka. Na ɓoye shi a wani ɗan tsumma. 21Na ji tsoronka, don kai mai wuyan sha’ani ne. Kakan ɗauki abin da ba ka ajiye ba, kakan kuma yi girbin abin da ba ka shuka ba.’
22 “Sai maigidansa, ya amsa ya ce, ‘Zan hukunta ka a kan kalmominka, kai mugun bawa! Ashe, ka san cewa ni mai wuyan sha’ani ne, nakan ɗauka abin da ban ajiye ba, ina kuma girbin abin da ban shuka ba? 23Don me ba ka sa kuɗina a wajen ajiya, don in na dawo, in sami riba a kai ba?’
24 “Sai ya ce wa waɗanda suke tsaye a wajen, ‘Ku karɓi minarsa ku ba wa wanda yake da mina goma.’
25 “Suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ai, yana da guda goma ko!’
26 “Ya amsa ya ce, ‘Ina gaya muku, duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Amma wanda ba shi da shi kuwa, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe. 27Amma waɗannan abokan gābana, waɗanda ba su so in zama sarkinsu ba, ku kawo su nan, ku karkashe su, a gabana.’ ”
Shiga mai nasara
(Mattiyu 21.1-11; Markus 11.1-11; Yohanna 12.12-19)
28Bayan Yesu ya yi wannan magana, sai ya yi gaba zuwa Urushalima. 29Da ya kai kusa da Betfaji da Betani, a tudun da ake kira Dutsen Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, ya ce musu, 30“Ku je ƙauyen da yake gaba da ku. Da kuna shiga, za ku tarar da wani ɗan jaki, wadda ba wanda ya taɓa hawa, a daure a wurin. Ku kunce shi ku kawo nan. 31In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke kunce shi?’ Ku ce masa, ‘Ubangiji yana bukatarsa.’ ”
32Waɗanda aka aika su yi gaba suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya gaya musu. 33Suna cikin kunce ɗan jakin, sai masu ɗan jakin suka ce musu, “Don me kuke kunce shi?”
34Suka amsa suka ce, “Ubangiji ne na bukatarsa.”
35Suka kawo shi wurin Yesu. Suka sa rigunarsu a kan ɗan jakin, sa’an nan suka sa Yesu a kai. 36Yana cikin tafiya, sai mutane suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya.
37Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa,
38“Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”
“Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!”
39Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce wa Yesu, “Malam, ka kwaɓi almajiranka!”
40Ya amsa ya ce, “Ina gaya muku, ko da sun yi shiru, duwatsu za su fara kirari.”
41Da ya yi kusa da Urushalima, ya kuma ga birnin, sai ya yi kuka a kanta, 42kuma ya ce, “In ke, ko ke ɗin ma, dā ma kin san abin da zai kawo miki salama a wannan rana, amma yanzu an ɓoye shi daga idanunki. 43Ranakun za su auko miki, a lokacin da abokan gābanki za su gina bango gāba da ke, su kuma kewaye inda kike, za su kuma tsare kowane gefenki, su sa ke a tsakiya. 44Za su fyaɗa ke a ƙasa, ke da ’ya’yan da suke cikin katanganki. Ba za su bar wani dutse a kan wani ba, saboda ba ki gane da lokacin da Allah zai ziyarce ki ba.”
Yesu a haikali
(Mattiyu 21.12-17; Markus 11.15-19; Yohanna 2.13-22)
45Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya. 46Ya ce musu, “A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’#19.46 Ish 56.7 amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”#19.46 Irm 7.11
47Kowace rana, ya yi ta koyarwa a haikalin. Amma manyan firistoci, da malaman dokoki, da shugabannin mutane, suna ƙoƙarin kashe shi. 48Amma ba su sami hanyar yin haka ba, domin kalmominsa sun kama hankalin dukan mutanen.
Pilihan Saat Ini:
Luka 19: SRK
Sorotan
Berbagi
Salin
Ingin menyimpan sorotan di semua perangkat Anda? Daftar atau masuk
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.