Yohanna 19
19
An yanke wa Yesu hukuncin mutuwar gicciye
1Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala. 2Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya. 3Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.
4Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.” 5Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!”
6Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!”
Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.”
7Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.”
8Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi, 9sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba. 10Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?”
11Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”
12Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.”
13Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata). 14Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida.
Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.”
15Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!”
Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?”
Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.”
16A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi.
Gicciyewa
(Mattiyu 27.32-44; Markus 15.21-32; Luka 23.26-43)
Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu. 17Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota). 18Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.
19Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne,
Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa.
20Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik. 21Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.”
22Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.”
23Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.
24Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci.”
Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce,
“Suka rarraba tufafina a junansu,
suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata.”#19.24 Zab 22.18
Abin da sojojin suka yi ke nan.
25To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. 26Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” 27ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
Mutuwar Yesu
(Mattiyu 27.45-56; Markus 15.33-41; Luka 23.44-49)
28Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, “Ina jin ƙishirwa.” 29To, akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hizzob, suka kai bakin Yesu. 30Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, “An gama.” Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.
31To, ranan nan fa, ranar Shirye-shirye ce, kashegari kuma muhimmin Asabbaci ne. Domin Yahudawa ba sa so a bar jikunan a kan gicciyoyi a Asabbaci, sai suka roƙi Bilatus a kakkarye ƙafafunsu kuma sauko da jikunan. 32Sai sojoji suka zo suka karya ƙafafun mutum na farko da aka gicciye tare da Yesu, da kuma na ɗayan. 33Amma sa’ad da suka zo kan Yesu suka tarar ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba. 34A maimako, sai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu a gefe da māshi, nan take jini da ruwa suka fito. 35Mutumin da ya gani ɗin shi ya ba da shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya san gaskiya yake faɗa, yana kuma ba da shaidar domin ku ma ku gaskata. 36Waɗannan abubuwa sun faru don a cika Nassi ne cewa, “Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da za a karya,”#19.36 Fit 12.46; Ƙid 9.12; Zab 34.20 37kuma kamar yadda wani Nassi ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”
Jana’izar Yesu
(Mattiyu 27.57-61; Markus 15.42-47; Luka 23.50-56)
38Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin. 39Yana tare da Nikodimus, wannan da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare. Nikodimus ya zo da mur da aloyes a gauraye, wajen awo ɗari. 40Da ɗaukowar jikin Yesu, sai su biyun suka nannaɗe shi tare da kayan ƙanshi a cikin ƙyallayen lilin bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza. 41A inda aka gicciye Yesu, akwai wani lambu, a cikin lambun kuwa akwai sabon kabari, wanda ba a taɓa sa kowa ba. 42Da yake ranan nan, ranar Shirye-shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka binne Yesu a can.
Pilihan Saat Ini:
Yohanna 19: SRK
Sorotan
Berbagi
Salin

Ingin menyimpan sorotan di semua perangkat Anda? Daftar atau masuk
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.