Luk 20

20
Ana Shakkar Izinin Yesu
(Mat 21.23-27; Mar 11.27-33)
1Wata rana yana koyar da mutane a Haikali, yana yi musu bishara, sai ga manyan firistoci da malaman Attaura, da shugabanni suka matso, 2suka ce masa, “Gaya mana da wane izini kake yin abubuwan nan, ko kuwa wa ya ba ka izinin?” 3Sai ya amsa musu ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku gaya mini, 4baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” 5Sai suka yi muhawwara da juna suka ce, “In mun ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 6In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ sai duk jama'a su jajjefe mu, don sun tabbata Yahaya annabi ne.” 7Sai suka amsa masa, suka ce, ba su san daga inda take ba. 8Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”
Misali na Manoman da suka Yi Ijarar Garkar Inabi
(Mat 21.33-46; Mar 12.1-12)
9 # Ish 5.1 Sai ya shiga ba jama'a misalin nan, ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya ba waɗansu manoma ijararta, ya kuma tafi wata ƙasa, ya daɗe. 10Da kakar inabi ta yi, ya aiki wani bawansa a gun manoman nan su ba shi gallar garkar. Amma manoman suka yi masa dūka, suka kore shi hannu wofi. 11Ya kuma aiki wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka wulakanta shi, suka kore shi hannu wofi. 12Har wa yau dai ya aiki na uku, shi kuwa suka yi masa rauni, suka kore shi. 13Sai mai garkar ya ce, ‘Me zan yi ke nan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana. Kila sa ga girmansa.’ 14Amma da manoman suka gan shi, suka yi shawara da juna suka ce, ‘Ai, wannan shi ne magajin. Mu kashe shi mana, gādon ya zama namu.’ 15Sai suka jefa shi a bayan shinge, suka kashe shi. To, me ubangijin garkan nan zai yi da su? 16Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.” Da suka ji haka, suka ce, “Allah ya sawwaƙe!” 17#Zab 118.22 Amma ya dube su, ya ce, “Wannan da yake a rubuce fa cewa,
“ ‘Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ne ya zama mafificin dutsen gini?’
18Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje, amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”
Biyan Haraji ga Kaisar
(Mat 22.15-22; Mar 12.13-17)
19Nan take malaman Attaura da manyan firistoci suka nema su kama Yesu, don sun lura a kansu ne ya ba da misalin, amma suna jin tsoron jama'a. 20Sai suka yi ta haƙwansa, suka aiki 'yan rahoto, su kuwa suka nuna kamar su masu adalci ne, da nufin su kama shi a maganarsa, su kuma ba da shi ga mai mulki ya hukunta shi. 21Suka tambaye shi suka ce, “Malam, ai, mun sani maganarka da koyarwarka duk gaskiya ne. Ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi. 22Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa babu?” 23Shi kuwa ya gane makircinsu, ya ce musu, 24“Ku nuna mini dinari. Surar wa da sunan wa yake a jikinsa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.” 25Sai ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” 26Sai suka kasa kama shi a kan wannan magana gaban mutane. Saboda kuma mamakin amsarsa, suka yi shiru.
Tambaya a kan Tashin Matattu
(Mat 22.23-33; Mar 12.18-27)
27 # A.M 23.8 Sai waɗansu Sadukiyawa suka zo wurinsa (su da suke cewa, ba tashin matattu), 28#M.Sh 25.5 suka tambaye shi suka ce, “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba ɗa, lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya. 29To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai. Na farko ya yi aure, ya mutu bai bar na baya ba. 30Na biyun, 31da na ukun kuma suka aure ta. Haka dai, duk bakwai ɗin suka aure ta, suka mutu, ba wanda ya bar ɗa. 32Daga baya kuma ita matar ta mutu. 33To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”
34Sai Yesu ya ce musu, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna aurarwa. 35Amma waɗanda aka ga sun cancanci samun shiga wancan zamani da kuma tashin nan daga matattu, ba za su yi aure ko aurarwa ba. 36Ba shi yiwuwa su sāke mutuwa, don daidai suke da mala'iku, 'ya'yan Allah ne kuwa, da yake 'ya'yan tashin matattu ne. 37#Fit 3.6 Game da tashin matattu kuwa, ai, Musa ma ya faɗa, a labarin kurmin, inda ya kira Ubangiji, Allahn Ibrahim, da Allahn Ishaku, da Allahn Yakubu. 38Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Don a wurinsa duka rayayyu ne.” 39Sai waɗansu malaman Attaura suka amsa suka ce, “Malam, ka faɗi daidai.” 40Daga nan kuma ba su yi ƙarfin halin tambayarsa wani abu ba.
Tambaya a kan Ɗan Dawuda
(Mat 22.41-46; Mar 12.35-37)
41Amma ya ce musu, “Ƙaƙa za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne? 42#Zab 110.1Domin Dawuda da kansa a Zabura ya ce,
“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
Zauna a damana,
43Sai na sa ka take maƙiyanka.’
44Dawuda ya ce shi Ubangiji ne. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?”
Yesu Ya Fallashi Malaman Attaura
(Mat 23.1-36; Mar 12.38-40; Luk 11.37-54)
45Ya ce wa almajiransa a gaban dukan jama'a, 46“Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo a cikin manyan riguna, masu so a gaishe su a kasuwa, masu son mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki. 47Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, masu yin doguwar addu'a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”

Chwazi Kounye ya:

Luk 20: HAU

Pati Souliye

Pataje

Kopye

None

Ou vle gen souliye ou yo sere sou tout aparèy ou yo? Enskri oswa konekte