Luk 19

19
Yesu da Zakka
1Yesu ya shiga Yariko. Yana ratsa garin, 2sai wani mutum mai suna Zakka, babba ne a cikin masu karɓar haraji, mai arziki ne kuma, 3ya nemi ganin ko wane ne Yesu, amma ya kasa ganinsa saboda taro, don shi gajere ne. 4Sai ya yi gaba a guje, ya hau wani durumi don ya gan shi, don Yesu ta nan zai bi. 5Da Yesu ya iso wurin, ya ɗaga kai ya ce masa, “Zakka, yi maza ka sauko, domin yau lalle a gidanka zan sauka.” 6Sai ya yi hanzari ya sauko, ya karɓe shi da murna. 7Da suka ga haka, duk suka yi ta gunaguni, suka ce, “A! A gidan mai zunubi dai ya sauka!” 8Sai Zakka ya miƙe, ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ka ga, rabin mallakata zan ba gajiyayyu. Kowa na zalunta kuwa, zan mayar masa da ninki huɗu.” 9Yesu ya ce masa, “Yau kam, ceto ya sauka a gidan nan, tun da yake shi ma ɗan Ibrahim ne. 10#Mat 18.11 Don Ɗan Mutum ya zo ne musamman garin neman abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”
Misali na Fam Goma
11Da suka ji abubuwan nan, Yesu ya ci gaba da gaya musu wani misali, gama yana kusa da Urushalima, suna kuma tsammani Mulkin Allah zai bayyana nan da nan. 12Sai ya ce, “Wani mutum mai asali ya tafi wata ƙasa mai nisa neman sarauta yă dawo. 13Sai ya kira bayinsa goma, ya ba su fam guda guda, ya kuma ce musu, ‘Ku yi ta jujjuya su har in dawo.’ 14Amma mutanensa suka ƙi shi, har suka aiki jakadu a bayansa, cewa ba sa so ya yi mulki a kansu. 15Ana nan, da ya samo sarautar ya dawo, sai ya yi umarni a kirawo bayin nan da ya bai wa kuɗin, ya ga ribar da suka ci a wajen jujjuyawar. 16Sai na farko ya zo gabansa, ya ce, ‘Ya ubangiji, fam ɗinka ya jawo fam goma.’ 17Sai shi kuma ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki! Tun da ka yi gaskiya a kan ƙaramin abu, to, na ba ka mulkin gari goma.’ 18Sai na biyun ya zo, ya ce, ‘Ya ubangida, fam ɗinka ya jawo fam biyar.’ 19Shi kuma ya ce masa, ‘Kai ma na ba ka mulkin gari biyar.’ 20Wani kuma ya zo, ya ce, ‘Ya ubangiji, ga fam ɗinka nan! Dā ma a mayani na ƙulle shi, na ajiye. 21Domin ina tsoronka, don kai mutum ne mai tsanani, son banza a gare ka, kakan girbi abin da ba kai ka shuka ba.’ 22Sai ya ce masa ‘Kai mugun bawa! Zan yi maka shari'a bisa ga abin da ka faɗa da bakinka. Ashe, ka sani ni mutum ne mai tsanani, mai son banza, ina kuma girbar abin da ba ni na shuka ba? 23To, in haka ne, don me ba ka ajiye kuɗin nawa a banki ba, da dawowata in ƙarɓa, har da riba?’ 24Sai ya ce wa na tsaitsaye a wurin, ‘Ku karɓe fam ɗin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan.’ 25Suka ce masa, ‘Ya ubangiji, ai, yana da fam goma.’ 26#Mat 13.12; Mar 4.25; Luk 8.18 ‘Ina dai gaya muku, duk mai abu a kan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai a karɓe masa. 27#Mat 25.14-30Waɗannan maƙiya nawa kuwa, da ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ ”
Mutanen Urushalima sun Marabci Yesu
(Mat 21.1-11; Mar 11.1-11; Yah 12.12-19)
28Da Yesu ya faɗi haka, ya yi gaba zuwa Urushalima. 29Da ya kusato Betafaji da Betanya, a wajen dutsen da ake kira Dutsen Zaitun, ya aiki almajiransa biyu, 30ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi. 31Kowa ya tambaye ku, ‘Don me kuke kwance shi?’ ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa.’ ” 32Sai waɗanda aka aika suka tafi, suka tarar kamar yadda ya faɗa musu. 33Suna cikin kwance aholakin, masu shi suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?” 34Sai suka ce, “Ubangiji ne yake bukatarsa.” 35Sai suka kawo shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa mayafansu a kan aholakin, suka ɗora Yesu. 36Yana cikin tafiya, sai mutane suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya. 37Da ya zo gab da gangaren Dutsen Zaitun, sai duk taron almajiran suka ɗauki murna, suna yabon Allah da murya mai ƙarfi saboda duk mu'ujizan da suka gani. 38#Zab 118.26 Suka ce, “Albarka ta tabbata ga Sarkin nan mai zuwa da sunan Ubangiji! Salama ta tabbata a Sama, ɗaukaka kuma ga Allah!” 39Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce masa, “Malam, ka kwaɓi almajiranka mana!” 40Ya amsa ya ce, “Ina dai gaya muku, ko waɗannan sun yi shiru, to, duwatsu ma sai su ɗauki sowa.”
41Da ya matso kusa, ya kuma hangi birnin, sai ya yi masa kuka, 42ya ce, “Da ma a ce a yanzu kun san abubuwan da suke kawo salama. Amma ga shi, a yanzu a ɓoye suke a gare ku. 43Don lokaci zai auko muku da maƙiyanku za su yi muku ƙawanya, su yi muku zobe, su kuma tsattsare ku ta kowane gefe, 44su fyaɗa ku a ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan'uwansa ba a birninku, don ba ku fahimci lokacin da ake sauko muku da alheri ba.”
Yesu Ya Tsabtace Haikali
(Mat 21.12-17; Mar 11.15-19; Yah 12.13-22)
45Sai ya shiga Haikali, ya fara korar masu sayarwa, 46#Ish 56.7; Irm 7.11 ya ce musu, “Ai, a rubuce yake cewa, ‘Ɗakina zai kasance ɗakin addu'a.’ Amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”
47 # Luk 21.37 Kowace rana ya yi ta koyarwa a Haikali. Amma manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka nema su hallaka shi. 48Suka kuwa rasa abin da za su yi, saboda maganarsa ta ɗauke wa duk jama'a hankali.

Chwazi Kounye ya:

Luk 19: HAU

Pati Souliye

Pataje

Kopye

None

Ou vle gen souliye ou yo sere sou tout aparèy ou yo? Enskri oswa konekte