Luk 16
16
Misali na Wakili Marar Gaskiya
1Ya kuma ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki da yake da wakili. Sai aka sari wakilin a wurinsa a kan yana fallasar masa da dukiya. 2Sai ya kira shi ya ce masa, ‘Labarin me nake ji naka? Kawo lissafin wakilcinka, don ba sauran ka zama wakilina.’ 3Sai wakilin ya ce a ransa, ‘Ƙaƙa zan yi, da yake maigida zai karɓe wakilci daga hannuna? Ga shi, ba ni da ƙarfin noma, in yi roƙo kuwa, ina jin kunya. 4Yauwa! Na san abin da zan yi, don in an fisshe ni daga wakilcin, mutane su karɓe ni a gidajensu.’ 5Sai ya kira mabartan maigidansa da ɗaya ɗaya, ya ce wa na farko, ‘Nawa maigida yake bin ka?’ 6Ya ce, ‘Garwa ɗari ta mai.’ Sai ya ce masa, ‘Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubutu hamsin,’ 7Ya kuma ce wa wani, ‘Kai fa, nawa ake binka?’ Sai ya ce, ‘Buhu ɗari na alkama.’ Ya ce masa, ‘Ga takardarka, ka rubuta tamanin.’ 8Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don 'yan zamani a ma'ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo. 9Ina gaya muku, ku yi abokai ta dukiya, ko da yake aba ce wadda take iya aikata mugunta, don sa'ad da ta ƙare su karɓe ku a gidaje masu dawwama.
10“Wanda yake da aminci a ƙaramin abu, mai aminci ne a babban abu. Wanda yake marar gaskiya a ƙaramin abu, marar gaskiya ne a babban abu. 11Idan fa ba ku yi aminci da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? 12In kuma ba ku yi aminci da kayan wani ba, wa zai ba ku halaliyarku? 13#Mat 6.24 Ba baran da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”
Shari'a da Mulkin Allah
14Farisiyawa kuwa da yake masu son kuɗi ne, da jin haka, suka yi masa tsaki. 15Sai ya ce musu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane. Amma Allah ya san zukatanku. Abin da mutane suke girmamawa ƙwarai, ai, abin ƙyama ne a gun Allah.
16 #
Mat 11.12,13 “Attaura da litattafan annabawa suna nan har ya zuwa ga Yahaya, daga lokacin nan kuwa ake yin bisharar Mulkin Allah, kowa kuma yana kutsawa zuwa ciki. 17#Mat 5.18 Duk da haka, zai fi sauƙi sararin sama da ƙasa su shuɗe, da ɗigo ɗaya na Attaura ya gushe.”
Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure
(Mat 19.1-12; Mar 10.1-12)
18 #
Mat 5.32; 1Kor 7.10,11 “Kowa ya saki mata tasa ya auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya ya yi zina.”
Mai Arziki da Li'azaru
19“An yi wani mai arziki, mai sa tufafin jan alharini da farare masu ƙawa, yana shan daularsa a kowace rana. 20An kuma ajiye wani gajiyayye a ƙofarsa, mai suna Li'azaru, wanda duk jikinsa miki ne. 21Shi kuwa yana marmarin ya ƙoshi da suɗin mai arzikin nan. Har ma karnuka sukan zo suna lasar miyakunsa. 22Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, mala'iku kuma suka ɗauke shi, suka kai shi wurin Ibraham. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. 23Yana a cikin Hades yana shan azaba, sai ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a wurinsa. 24Sai ya yi kira ya ce, ‘Baba Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiko Li'azaru ya tsoma kan yatsarsa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.’ 25Amma Ibraham ya ce, ‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li'azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba. 26Banda wannan ma duka, tsakaninmu da ku akwai wani gawurtaccen rami mai zurfi, zaunanne, don waɗanda suke son ƙetarewa zuwa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ƙetaro zuwa wurinmu daga can.’ 27Sai mai arzikin ya ce, ‘To, ina roƙonka, Baba, ka aika shi zuwa gidan ubana, 28don ina da 'yan'uwa biyar maza, ya je ya yi musu gargaɗi, kada su ma su zo wurin azabar nan.’ 29Amma Ibrahim ya ce, ‘Ai, suna da littattafan Musa da na annabawa, su saurare su mana.’ 30Sai ya ce, ‘A'a, Baba Ibrahim, in dai wani daga cikin matattu ya je wurinsu sa tuba.’ 31Ibrahim ya ce masa, ‘In dai har ba su saurari littattafan Musa da na annabawa ba, ko da wani ya tashi daga cikin matattu ma, ba za su rinjayu ba.’ ”
Chwazi Kounye ya:
Luk 16: HAU
Pati Souliye
Pataje
Kopye
Ou vle gen souliye ou yo sere sou tout aparèy ou yo? Enskri oswa konekte
@Bible Society of Nigeria 1979