अनुग्रह का गाननमूना

अनुग्रह का गान

दिन 3 का 5

Ina Ubangiji yake lokacin da rayuwa ta tsananta?

Idan kun taɓa yin mamakin hakan, to kuna cikin tarayya mai kyau. Na yi tambaya iri ɗaya. Haka yana da kyau sosai ga kowane ɗan adam. Lokacin da rayuwa ta juya maka baya - lokacin da ake ganin kana fuskantar cikas hagu zuwa dama - halinmu shi ne mu yi kuka, "Ina kake, Ubangiji?"

Kuma amsar da aka bayar tana ɗaya daga cikin mafi kyawun abubuwan da za ku taɓa ji.

Romans 8:38–39 ta ce,

“Domin na tabbata ba mutuwa ko rayuwa ba, ba mala’iku ba aljanu, ba na yanzu ba na nan gaba, ba wani iko, ba tsawo ba zurfi, ba wani abu cikin dukkan halitta, zai iya raba mu da ƙaunar Ubangiji wannan ya na wajen Yesu Almasihu.”

To, bisa ga wannan nassi, ina Ubangiji yake lokacin da rayuwa ta yi tsananta? Ina yake lokacin da abokanku suka bar ku? Ko lokacin da danginku suka rabu? Ko lokacin da mafarkinka ya zo ya rushe?

Littafin Linjila ya ce Ubangiji Ya na nan tare da kai a lokacin ɓacin ranka - yana ƙaunar ka ciki duka.

Yanzu, wataƙila kuna tunani, "Wannan yana da kyau ... amma dai me ya sa ba ya kawar min da ɓacin rai na?"

Babbar tambaya. Wannan shi ne wani abin da mutane da yawa suka tambaya. Kamar Fada Paul, wanda ya rubuta maƙalar da ke sama.

Paul ya jure baƙin ciki da yawa da wahala cikin ƴan shekaru kaɗan fiye da yadda yawancin mutane ke fuskanta a rayuwa. An yi masa duka, an yi masa isgili, aka ɓata shi, kuma an ɗaure shi. Ya rasa abokai ta hanyar mutuwa, ya fuskanci kaɗaici, kuma ya yi kokawa da cutar damuwa. Daga bisani, shi kanshi Paul an kashe a kan bin Yesu.

A wani lokaci Paul ya na fuskantar mawuyacin hali na musamman. Ba mu san yadda abin yake ba, amma ya kwatanta shi a matsayin ƙaya a cikin jikinsa. Wataƙila ciwo ne, taɓin hankali, ko ciwo mai tsanani. Ko ma mene, bai iya girgiza shi ba, kuma ya roƙi Ubangiji da ya ɗauke shi.

Ubangiji Ya amsa...

"Alherina ya ishe ku, domin ikona ya cika cikin rauni." (2 Corinthians 12:9)

Me Ubangiji yake nufi da haka? Bai damu da cewa Paul yana fama ba ne?

Tabbas Yana yi. Kamar yadda ya damu da zafin ciwonku rayuwa. Kada ku manta cewa Yesu mutum ne “wanda ya saba da ciwo” kamar yadda aka faɗa a Ishaya 53:3. Ya san bakin ciki. Yana fuskance ku. Yana son ku.

Amma mafi girman abin da muke buƙata ni da ku - kuma abin da wannan duniyar ta fi buƙata - ba sauyin yanayi ba ne, amma se dai canji na zuciya.

Abin da Yesu ya yi ke nan lokacin da ya zo cikin rayuwar ku. Kuma wannan shi ne fatan da yake nunawa a rayuwarku lokacin da ya ɗauke ku cikin rauni maimakon ya cece ka daga gare shi.

Ya ce, "Zan taimakeku cikin wannan. Zan gyara ku ta wannan. Kuma zan yi amfani da ku don nuna alherina ga duniyar da ke buƙatata fiye da komai."

Don haka kowace irin wahala, baƙin ciki, ko ɓacin ran da kuke fuskanta a yau, samu kwanciyar hankali a cikin alƙawarin Ubangiji na cewa ba zai taɓa barin ku ba, babu abin da zai raba ku da ƙaunarsa wajen Yesu, kuma alherinsa shi ne kawai kuke buƙata. Sannan za ku iya yin waƙa da ƙwarin gwiwa...

Ta hanyar haɗari da yawa, wahalhalu da tarkoki.

Na rifa na zo;

Alherin ya kawo ni lafiya har zuwa yanzu,

Kuma alheri ne zai kai ni gida.

Albarka,

—Nick Hall

दिन 2दिन 4

इस योजना के बारें में

अनुग्रह का गान

विवरण इस भक्तिमय अनुग्रह गान के माध्यम से आपके प्रति ईश्वर के प्रेम की गहराई का पता लगाएं। इंजीलवादी निक हॉल आपको 5-दिवसीय शक्तिशाली भक्ति के माध्यम से मार्गदर्शन करेगा जो आपको आपके ऊपर गाए गए ईश्वर की कृपा के गान में शामिल होने के लिए आमंत्रित करेगा।

More

हम यह योजना प्रदान करने के लिए PULSE Outreach को धन्यवाद देना चाहते हैं। और अधिक जानकारी के लिए कृपया विजिट करें: https://anthemofgrace.com/