अनुग्रह का गाननमूना

अनुग्रह का गान

दिन 1 का 5

"Ta yaya wani zai iya so na?"

Ka taɓa tunanin wani abu kamar haka? Na taɓa.

Lokacin da nake girma, na yi nisa da kamala. Har yanzu haka nake. Amma a matsayin matashi, na ɗauki laifi da yawa da abin kunya. Mutane na faɗa min abubuwa kamar "Ubangiji ya na sonka" ko " Ya na da wani abin da ya tsara maka a rayuwarka."

Shi ya sa nake son labarin waƙar "Alheri mai ban mamaki."

Yaya daɗin sautin Alheri mai ban mamaki,

Wannan da ya ceci lalatacce kamar ni!

Da na taɓa ɓata, amma yanzu na samu;

Da ni makaho ne, amma yanzu ina gani.

Ko kun shafe lokaci a coci ko a'a, tabbas kun san wannan waƙar. A matsayin ɗaya daga cikin mafi yawan waƙoƙin da aka yi rikodin a tarihi, "Alheri mai ban Mamaki" Elvis, Aretha Franklin, da Bono sun yi ta. An rera ta lokacin da Nelson Mandela ya samu jagoranci har ma an nuna a shirinsu Simpsons!

Amma abin da ba za ku sani ba shi ne cewa wani kyaftin ɗin jirgin ruwan bayi da aka yi a ƙarni na sha takwas mai suna John Newton ne ya rubuta waƙar "Alheri mai ban Mamaki".

Newton ya yi sunan da zai sa a ga yawancin mu da kyau ta hanyar kwatance. Kuna tsammanin kun yi kusakurai? Kuna tunanin kuna da datti? Hannuwan Newton sun ɗauki laifin cinikin rayuwar ɗan adam don riba.

To ta yaya wannan mutumin zai iya rubuta waƙa don murnar nuna ƙaunar da Ubangiji yake masa?

Amsar ita ce Rahama.

Labari mai kyau game da Yesu Almasihu shi ne ku da ni ba za mu iya tsarkake kanmu da ya isa mu samu ƙaunar Ubangiji ba. Yana ga duk da an san abu mafi muni akanmu, Ubangiji yana kusantarmu da so domin ya tseratar da mu daga daga zunubanmu.

Romans 5:8 tana cewa kamar haka: “Amma cikin wannan Ubangiji yana nuna ƙaunarsa gare mu; Tun muna masu zunubi, Yesu ya mutu dominmu. (NIV)

John Newton ya kwashe shekaru yana izgili ga alherin Ubangiji. Zai ji abubuwa iri ɗaya game da ƙaunar Ubangiji da na girma ina ji. Wataƙila har abubuwan da kuka ji ma. Amma ya kasa yarda da hakan… ba ya so ya yarda da shi.

Sannan wata rana da daddare yayin da yake tuƙa jirgin ruwan bayinsa cikin wata guguwa mai ƙarfi, ya yi kuka ga Ubangiji domin samun jinƙai. Yayin da jirgin ruwansa ya wuce lafiya, a ƙarshe sai ya ba da gaskiya ga Yesu kuma ya samu alherin da ya ƙi na dogon lokaci.

Daga baya, Newton ya taka rawa wajen kawo ƙarshen cinikin bayi a Burtaniya. Sai ya zama mai wa’azi, ya kula da talakawa, kuma ya yi ƙaurin suna a matsayin fasto wanda ya haɗa mutane daga kowane fanni na rayuwa tare.

Alherin Ubangiji ba kawai ya ceci Newton ba ne, ya kuma canza Newton.

Amma duk yadda Newton ya girma a cikin dangantakarsa da Ubangiji, bai manta ba cewa duk saboda alheri ne. Zunubinsa ya cancanci hukunci. Namu ma ya isa. Amma ƙaunar Ubangiji ta sa shi ya kwaranyar da hukunci a kan Yesu, wanda da son ransa ya ɗauki matsayinmu akan gicciye. Wannan alheri ne mai ban mamaki.

Newton ya ce a ƙarshen rayuwa...

Na tuna abubuwa biyu: cewa ni babban mai zunubi ne - kuma Almasihu babban mai ceto ne!

To, duk wannan laifi da kunya fa? Ya batun kusakurenku fa? Ya batun waɗancan abubuwan da kuka yi ko kuka faɗa a baya waɗanda kuke fatan dama za ku iya dawo da su? Ba za a iya son ku ba ne? Shin zunubinka ya fi ƙarfin alherin Ubangiji?

Bari mu ɗauki darasi daga Newton a yau kuma mu huta daga gaskiyar cewa ƙaunar Ubangiji ba ta dogara da ƙimarmu ba, kuma alherinsa ya fi isa ya ceci miyagu kamar ni.

Albarkoki,

--Nick Hall

पवित्र शास्त्र

दिन 2

इस योजना के बारें में

अनुग्रह का गान

विवरण इस भक्तिमय अनुग्रह गान के माध्यम से आपके प्रति ईश्वर के प्रेम की गहराई का पता लगाएं। इंजीलवादी निक हॉल आपको 5-दिवसीय शक्तिशाली भक्ति के माध्यम से मार्गदर्शन करेगा जो आपको आपके ऊपर गाए गए ईश्वर की कृपा के गान में शामिल होने के लिए आमंत्रित करेगा।

More

हम यह योजना प्रदान करने के लिए PULSE Outreach को धन्यवाद देना चाहते हैं। और अधिक जानकारी के लिए कृपया विजिट करें: https://anthemofgrace.com/