Logo YouVersion
Îcone de recherche

Mar 3

3
Mai Shanyayyen Hannu
(Mat 12.9-14; Luk 6.6-11)
1Sai ya sāke shiga majami'a. Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. 2Sai suka yi haƙwansa su ga ko zai warkar da shi ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa. 3Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Fito nan fili.” 4Ya ce musu, “Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko kuwa mugunta? A ceci rai, ko kuwa a kashe shi?” Amma sai suka yi shiru. 5Da ya duddube su da fushi, yana baƙin ciki da taurin zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. 6Da Farisiyawa suka fita, nan da nan suka yi shawara da mutanen Hirudus a kansa, yadda za su hallaka shi.
Taro Mai Yawa a Bakin Teku
7Sai Yesu ya tashi tare da almajiransa, suka je bakin tekun. Taro mai yawan gaske kuwa daga ƙasar Galili ya biyo shi, har ma daga ƙasar Yahudiya, 8da Urushalima, da ƙasar Edom, da hayin Kogin Urdun, da kuma wajen Taya da Sidon, babban taro ya zo wurinsa, don sun ji labarin duk abin da yake yi. 9#Mar 4.1; Luk 5.1-3Don gudun kada taron ya mammatse shi kuwa, sai ya ce wa almajiransa su keɓe masa ƙaramin jirgi guda, 10saboda ya riga ya warkar da mutane da yawa, har ya kai ga duk masu cuta na dannowa wurinsa domin su taɓa shi. 11Baƙaƙen aljannu kuwa, duk sa'ad da suka gan shi, sai su fāɗi gabansa suna kururuwa, suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne.” 12Sai ya kwaɓe su ƙwarai kada su bayyana shi.
Yesu Ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu
(Mat 10.1-4; Luk 6.12-16)
13Ya hau dutse, ya kira waɗanda yake so, suka je wurinsa. 14Ya zaɓi mutum goma sha biyu su zauna tare da shi, ya riƙa aikensu suna wa'azi. 15Ya kuma ba su ikon fitar da aljannu. 16Ga waɗanda ya zaɓa, Bitrus, 17da Yakubu ɗan Zabadi, da kuma ɗan'uwansa Yahaya, ya sa musu suna Buwanarjis, wato 'ya'yan tsawa. 18Sai kuma Andarawas, da Filibus, da Bartalamawas, da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza, da Saminu Bakan'ane, 19da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bāshe shi.
Yesu da Ba'alzabul
(Mat 12.22-32; Luk 11.14-23)
Sa'an nan ya shiga wani gida. 20Taron kuwa ya sāke haɗuwa har ya hana su cin abinci. 21Da 'yan'uwansa suka ji haka, sai suka fita su kamo shi, saboda sun ce, “Ai, ya ruɗe.” 22#Mat 9.34; 10.25 Malaman Attaura kuwa da suka zo daga Urushalima sai suka ce, “Ai, Ba'alzabul ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.” 23Sai Yesu ya kira su, ya ba su misali da cewa, “Ina Shaiɗan zai iya fitar da Shaiɗan? 24Ai, in mulki ya rabu a kan gāba, wannan mulki ba zai ɗore ba. 25Haka in gida ya rabu a kan gāba, wannan gida ba zai ɗore ba. 26Shaiɗan kuma in ya tayar wa kansa, ya rabu, ba zai ɗore ba, ƙarewa tasa ce ta zo. 27Ba mai iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum ya washe kayansa, sai ko ya fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin, sa'an nan kuma ya washe gidansa.
28“Hakika, ina gaya muku, ā gafarta wa 'yan adam duk zunubansu, da kowane saɓon da suka hurta, 29#Luk 12.10 amma fa, duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki ba ya samun gafara har abada, ya yi madawwamin zunubi ke nan.” 30Wannan kuwa don sun ce, “Yana da baƙin aljan ne.”
Uwar Yesu da 'Yan'uwansa
(Mat 12.46-50; Luk 8.19-21)
31Sa'an nan uwa tasa da 'yan'uwansa suka zo. Suna tsaye a waje, sai suka aika masa yă je. 32Tar o kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna nemanka a waje.” 33Ya amsa musu ya ce, “Su wane ne tsohuwata da 'yan'uwana?” 34Sai ya waiwayi waɗanda suke zaune kewaye da shi, ya ce, “Ga tsohuwata a nan da 'yan'uwana! 35Ai, kowa ya yi abin da Allah yake so, shi ne ɗan'uwana, ita ce 'yar'uwata, ita ce kuma tsohuwata.”

Sélection en cours:

Mar 3: HAU

Surbrillance

Partager

Copier

None

Tu souhaites voir tes moments forts enregistrés sur tous tes appareils? Inscris-toi ou connecte-toi