Logo YouVersion
Îcone de recherche

Mar 11

11
Mutanen Urushalima Sun Marabci Yesu
(Mat 21.1-11; Luk 19.28-40; Yah 12.12-19)
1Da suka kusato Urushalima, da Betafaji, da Betanya, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu, 2ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi. 3Kowa ya ce muku, ‘Don me kuke haka?’ ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa, Zai kuma komo da shi nan da nan.’ ” 4Sai suka tafi, suka tarar da aholakin a ɗaure a ƙofar gida a bakin hanya, suka kwance shi. 5Sai waɗanda suke tsaitsaye a gun suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?” 6Suka faɗa musu abin da Yesu ya ce. Su kuwa suka ƙyale su suka tafi. 7Suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfiɗa mayafansu a kai, ya hau. 8Sai mutane da yawa suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka baza ganyen da suka kakkaryo a saura. 9#Zab 118.25,26 Da na gaba da na baya suka riƙa sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! 10Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na ubanmu Dawuda! Hosanna ga Allah!”
11Sai ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Da dai ya dudduba kome, da yake magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyun nan.
La'antar da Itacen Ɓaure
(Mat 21.18-19)
12Kashegari da suka tashi daga Betanya, ya ji yunwa. 13Da ya hango wani itacen ɓaure mai ganye kore shar, sai ya je ya ga ko ya sami 'ya'ya. Da ya isa wurinsa bai ga kome ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan ɓaure ba ne. 14Sai ya ce wa ɓauren, “Kada kowa ya ƙara cin 'ya'yanka har abada!” Almajiransa kuwa suna ji.
Yesu Ya Tsabtace Haikalin
(Mat 21.12-17; Luk 19.45-48; Yah 2.13-22)
15Suka iso Urushalima. Ya shiga Haikalin ya fara korar masu saye da sayarwa daga ciki, ya kuma birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai, 16ya kuma hana kowa ratsa Haikalin ɗauke da wani abu. 17#Ish 56.7; Irm 7.11 Sai ya yi musu gargaɗi ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira masujadata ɗakin addu'a na dukkan al'ummai’? Amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.” 18Da manyan firistoci da malaman Attaura suka ji wannan magana suka kuma nemi hanyar hallaka shi, saboda sun tsorata da shi, don duk jama'a na mamaki da koyarwa tasa. 19Kowace yamma kuwa Yesu yakan fita gari.
Aya a kan Bushewar Itacen Ɓaure
(Mat 21.20-22)
20Suna wucewa da safe, sai suka ga ɓauren nan ya bushe har saiwarsa. 21Bitrus kuwa ya tuna, sai ya ce masa, “Ya Shugaba, dubi! Ɓauren nan da ka la'anta ya bushe!” 22Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku gaskata da Allah. 23#Mat 17.20; 1Kor 13.2 Hakika, ina gaya muku, kowa ya ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku’, bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata abin da ya faɗa zai auku, sai a yi masa shi. 24Don haka ina dai gaya muku, kome kuka roƙa da addu'a, ku gaskata cewa samamme ne, za ku kuwa samu. 25#Mat 6.14,15 Koyaushe kuka tsaya yin addu'a, in akwai wanda kuke jin haushinsa, ku yafe masa, domin Ubanku da yake Sama shi ma yă yafe muku laifofinku. 26[Amma in ba kwa yafewa, haka Ubanku da yake Sama ma ba zai yafe muku laifofinku ba.]”
Ana Shakkar Iznin Yesu
(Mat 21.23-27; Luk 20.1-8)
27Suka koma Urushalima. Yana zaga cikin Haikalin sai manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka zo wurinsa, 28suka ce masa, “Da wane izni kake yin waɗannan abubuwa, ko kuwa wa ya ba ka iznin yin haka?” 29Sai Yesu ya ce musu, “Zan yi muku wata tambaya. Ku ba ni amsa, ni kuwa in gaya muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan. 30To, baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce? Ku ba ni amsa.” 31Sai suka yi muhawara da juna, suka ce, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 32Ma kuwa ce, ‘Ta mutum ce’?” Suna kuwa jin tsoron jama'a, don duk kowa ya tabbata, cewa Yahaya annabi ne. 33Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan ba.”

Sélection en cours:

Mar 11: HAU

Surbrillance

Partager

Copier

None

Tu souhaites voir tes moments forts enregistrés sur tous tes appareils? Inscris-toi ou connecte-toi