Logo YouVersion
Îcone de recherche

Mar 1

1
Wa'azin Yahaya Maibaftisma
(Mat 3.1-12; Luk 3.1-9,15-17; Yah 1.19-28)
1Farkon bisharar Yesu Almasihu, Ɗan Allah, ke nan. 2#Mal 3.1 Yadda yake a rubuce a littafin Annabi Ishaya cewa,
“Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,
Wanda zai shirya maka hanya.
3 # Ish 40.3 Muryar mai kira a jeji tana cewa,
Ku shirya wa Ubangiji tarfarki,
Ku miƙe hanyoyinsa.”
4Yahaya Maibaftisma ya bayyana a jeji, yana wa'azi mutane su tuba a yi musu baftisma domin a gafarta musu zunubansu. 5Sai duk mutanen ƙasar Yahudiya, da dukan mutanen Urushalima suka yi ta zuwa wurinsa, suna bayyana zunabansu, yana yi musu baftisma a Kogin Urdun. 6#2Sar 1.8 Yahaya kuwa na sanye da tufar gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma. 7Ya yi wa'azi ya ce, “Wani na zuwa bayana wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in sunkuya in ɓalle ba. 8Ni da ruwa na yi muku baftisma, amma shi da Ruhu Mai Tsarki zai yi muku.”
An Yi wa Yesu Baftisma
(Mat 3.13-17; Luk 3.21-22)
9Sai ya zamana a wannan lokaci Yesu ya zo daga Nazarat ta ƙasar Galili. Yahaya ya yi masa baftisma a Kogin Urdun. 10Da fitowarsa daga ruwan sai ya ga sama ta dāre, Ruhu yana sauko masa kamar kurciya. 11#Far 22.2; Zab 2.7; Ish 42.1; Mat 3.17; 12.18; Mar 9.7; Luk 3.22 Aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai.”
Shaiɗan Ya Gwada Yesu
(Mat 4.1-11; Luk 4.1-13)
12Nan da nan sai Ruhu ya iza shi jeji. 13Yana jeji har kwana arba'in, Shaiɗan na gwada shi, yana tare da namomin jeji, mala'iku kuma suna yi masa hidima.
Yesu Ya Fara Aiki a Galili
(Mat 4.12-17; Luk 4.14-15)
14To, bayan an tsare Yahaya, sai Yesu ya shigo ƙasar Galili, yana yin bisharar Allah, 15#Mat 3.2 yana cewa, “Lokaci ya yi, Mulkin Allah ya kusato. Ku tuba, ku gaskata da bishara.”
Yesu Ya Kira Masunta Huɗu
(Mat 4.18-22; Luk 5.1-11)
16Yana wucewa ta bakin Tekun Galili, sai ya ga Bitrus da Andarawas ɗan'uwansa, suna jefa taru a teku, don su masunta ne. 17Yesu ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.” 18Nan da nan kuwa suka watsar da tarunansu, suka bi shi. 19Da ya ci gaba kaɗan, sai ya ga Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirginsu suna gyaran taruna. 20Nan da nan da ya kira su, suka bar ubansu Zabadi a cikin jirgin tare da ma'aikata, suka bi shi.
Mai Baƙin Aljan
(Luk 4.31-37)
21Suka shiga Kafarnahum. Ran Asabar kuwa, ya shiga majami'a yana koyarwa. 22#Mat 7.28,29 Sun yi mamakin koyarwa tasa, domin yana koya musu da hakikan cewa, ba kamar malaman Attaura ba. 23Nan take sai ga wani mutum mai baƙin aljan a majami'arsu, yana ihu, 24yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.” 25Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Yi shiru! Rabu da shi!” 26Sai baƙin aljanin ya buge shi, jikinsa na rawa, ya yi ihu, ya rabu da shi. 27Duk suka yi mamaki, har suka tanttambayi juna suna cewa, “Kai, mene ne haka? Tabɗi! Yau ga baƙuwar koyarwa! Har baƙaƙen aljannu ma yake yi wa umarni gabagaɗi, suna kuwa yi masa biyayya!” 28Nan da nan sai ya shahara a ko'ina duk kewayen ƙasar Galili.
Yesu ya Warkar da Surukar Bitrus
(Mat 8.14-15; Luk 4.38-39)
29Da fitarsu daga majami'a, sai suka shiga gidan su Bitrus da Andarawas, tare da Yakubu da Yahaya. 30Surukar Bitrus kuwa na kwance tana zazzaɓi, nan da nan suka ba shi labarinta. 31Sai ya matso, ya kama hannunta, ya tashe ta, zazzaɓin kuwa ya sake ta, har ta yi musu hidima.
Yesu Ya Warkar da Mutane da yawa da Maraice
(Mat 8.16-17; Luk 4.40-41)
32Da magariba, bayan faɗuwar rana, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya, da masu aljannu. 33Sai duk garin ya haɗu a ƙofar gidan. 34Ya warkar da marasa lafiya da yawa, masu cuta iri iri, ya kuma fitar wa mutane aljannu da yawa. Bai ko yarda aljannun su yi wata magana ba, domin sun san shi.
Yesu Ya Tafi Yin Wa'azi
(Luk 4.42-44)
35Da asussuba ya tashi ya fita, ya tafi wani wuri inda ba kowa, ya yi addu'a a can. 36Sai Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka bi shi. 37Da suka same shi, suka ce masa, “Duk ana nemanka.” 38Ya ce musu, “Mu tafi garuruwan da suke gaba, in yi wa'azi a can kuma, domin saboda haka ne na fito.” 39#Mat 4.23; 9.35 Ya gama ƙasar Galili duk yana wa'azi a majami'unsu, yana kuma fitar wa mutane aljannu.
Yesu Ya Warkar da Kuturu
(Mat 8.1-4; Luk 5.12-16)
40Wani kuturu ya zo wurinsa, yana roƙonsa, yana durƙusawa a gabansa, yana cewa, “In ka yarda kana da iko ka tsarkake ni.” 41Da tausayi ya kama Yesu, sai ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce masa, “Na yarda, ka tsarkaka.” 42Nan take sai kuturtar ta rabu da shi, ya tsarkaka. 43Ya kwaɓe shi ƙwarai, ya sallame shi nan da nan, 44#L.Fir 14.1-32 ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka saboda tsarkakewarka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.” 45Amma ya tafi, ya shiga sanar da maganar, yana baza labarin al'amarin ko'ina, har ya zamana Yesu bai ƙara shiga wani gari a sarari ba, sai ya zauna a waje a wuraren da ba kowa. Mutane kuwa suka yi ta zuwa wurinsa daga ko'ina.

Sélection en cours:

Mar 1: HAU

Surbrillance

Partager

Copier

None

Tu souhaites voir tes moments forts enregistrés sur tous tes appareils? Inscris-toi ou connecte-toi