Luk 22

22
An Ƙulla Shawara gāba da Yesu
(Mat 26.1-5,14-16; Mar 14.1-2,10-11; Yah 11.45-53)
1 # Fit 12.1-27 To, idin abinci marar yisti, wanda ake ce da shi Idin Ƙetarewa, ya gabato. 2Sai manyan firistoci da malaman Attaura suka yi ta neman yadda za su kashe shi, amma kuwa suna tsoron jama'a.
3Sai Shaiɗan ya shiga Yahuza, wanda ake kira Iskariyoti, ɗaya daga cikin sha biyun nan. 4Sai ya tafi ya yi shawara da manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali a kan yadda zai bāshe shi a gare su. 5Sai suka yi murna, suka kuma yi alkawarin ba shi kuɗi. 6Shi kuwa ya yarda, ya kuma nemi hanyar bāshe shi a gare su bayan idon jama'a.
Yesu Ya Ci Jibin Ƙetarewa tare da Almajiransa
(Mat 26.17-25; Mar 14.12-21; Yah 13.21-30)
7Sai ranar idin abinci marar yisti ta zo, wato, rana da ake yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa. 8Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce musu, “Ku je ku shirya mana Jibin Ƙetarewa mu ci.” 9Suka ce masa, “Ina kake so mu shirya?” 10Ya ce musu, “Ga shi, da shigarku gari, za ku gamu da wani mutum ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi har zuwa cikin gidan da ya shiga. 11Ku ce wa maigidan, ‘Malam ya ce, ina masaukin da zai ci Jibin Ƙetarewa da almajiransa?’ 12Shi kuwa zai nuna muku wani babban soron bene mai kaya a shirye. A nan za ku shirya mana.” 13Sai suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Jibin Ƙetarewa.
Cin Jibin Ubangiji
(Mat 26.26-30; Mar 14.22-26; 1Kor 11.23-26)
14Da lokaci ya yi, sai ya zauna cin abinci, manzanninsa kuma suna tare da shi. 15Ya ce musu, “Ina so ƙwarai ko dā ma in ci jibin nan na Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wuya. 16Gama ina gaya muku ba zan ƙara cin sa ba, sai an cika shi a Mulkin Allah.” 17Sai ya karɓi ƙoƙo, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya ce, “Ungo wannan, ku shassha. 18Ina gaya muku, daga yanzu, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai Mulkin Allah ya bayyana.” 19Sai ya ɗauki gurasa, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka, domin tunawa da ni.” 20#Irm 31.31-34 Haka kuma, bayan jibi, ya ɗauki ƙoƙon, ya ce, “Ƙoƙon nan sabon alkawari ne, da aka tabbatar da jinina da za a bayar dominku. 21#Zab 41.9 Amma ga shi, mai bashe ni ɗin nan yana ci a akushi ɗaya da ni. 22Lalle Ɗan Mutum zai ƙaura kamar yadda aka ƙaddara, duk da haka, kaiton mutumin nan da yake ba da shi!” 23Sai suka fara tambayar juna ko wane ne a cikinsu zai yi haka.
Mūsū a kan Ko wane ne Babba
24 # Mat 18.1; Mar 9.34; Luk 9.46 Sai musu ya tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne babbansu. 25Sai ya ce musu, “Sarakunan al'ummai sukan nuna musu iko, mahukuntansu kuma sukan nema a ce da su, ‘Mataimakan jama'a.’ 26#Mat 23.11; Mar 9.35#Mat 20.25-27; Mar 10.42-44 Amma ku kam ba haka ba. Sai dai wanda yake babba a cikinku yă zama kamar ƙarami, shugaba kuwa yă zama kamar mai hidima. 27#Yah 13.12-15 Wa ya fi girma? Wanda ya zauna cin abinci, ko kuwa mai hidimar? Ashe, ba wanda ya zauna cin abinci ba ne? Ga shi kuwa, ina a cikinku kamar mai hidima.
28“Ku ne kuka tsaya gare ni a gwaje-gwajen da na sha. 29Kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka, ni ma nake ba ku iko, 30#Mat 19.28 ku ci ku sha tare da ni a mulkina, ku kuma zauna a kursiyai, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila.
Bitrus zai yi Mūsun Sanin Yesu
(Mat 26.31-35; Mar 14.27-31; Yah 13.36-38)
31“Bitrus, ya Bitrus, Shaiɗan ya nemi izinin sheƙe ku kamar alkama, ya kuwa samu. 32Ni kuwa na yi maka addu'a, kada bangaskiyarka ta kāsa. Kai kuma, bayan da ka juyo, sai ka ƙarfafa 'yan'uwanka.” 33Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, a shirye nake in bi ka har cikin kurkuku, ko kuma Lahira.” 34Yesu ya ce, “Ina dai gaya maka Bitrus, a yau ma, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”
Jakar Kuɗi, Burgami da Takobi
35 # Mat 10.9,10; Mar 6.8,9; Luk 9.3; 10.4 Ya kuma ce musu, “Sa'ad da na aike ku ba kuɗi a ɗamararku, ba burgami, ba takalma, akwai abin da kuka rasa?” Suka ce, “Babu.” 36Ya ce musu, “Amma a yanzu duk mai jakar kuɗi yă ɗauka, haka kuma mai burgami. Wanda kuwa ba shi da takobi, ya sayar da mayafinsa ya saya. 37#Ish 53.12 Ina dai gaya muku, lalle ne a cika wannan Nassi a kaina cewa, ‘An lasafta shi a cikin masu laifi.’ Gama abin da aka faɗa a kaina, tabbatarsa ta zo.” 38Sai suka ce, “Ya Ubangiji, ai, ga takuba biyu.” Ya ce musu, “Ya isa.”
Yesu Ya Yi Addu'a a Gatsemani
(Mat 26.36-46; Mar 14.32-42)
39Sai ya fita ya tafi Dutsen Zaitun, kamar yadda ya saba. Almajiransa kuwa suka bi shi. 40Da ya iso wurin, ya ce musu, “Ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji.” 41Sai ya ɗan rabu da su misalin nisan jifa, ya durƙusa, ya yi addu'a. 42Ya ce, “Ya Uba, in dai ka yarda, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai, ba nufina ba, sai naka za a bi” 43[Sai wani mala'ika ya bayyana a gare shi daga Sama, yana ƙarfafa shi. 44Domin kuma yana shan wahala gaya, sai ya ƙara himmar addu'a, har jiɓinsa yana ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.] 45Da ya tashi daga addu'a, ya koma wurin almajiran, ya tarar suna barci saboda baƙin ciki. 46Sai ya ce musu, “Don me kuke barci? Ku tashi, ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji.”
An Ba da Yesu, an Kama Shi
(Mat 26.47-56; Mar 14.43-50; Yah 18.2-11)
47Kafin ya rufe baki, sai ga taron jama'a suka zo, mutumin da ake kira Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, yake musu jagaba. Sai ya matso kusa da Yesu, don ya sumbace shi. 48Amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, ashe, da sumba za ka ba da Ɗan Mutum?” 49Da na kusa da shi suka ga abin da za a yi, suka ce, “Ya Ubangiji, mu yi sara da takuba ne?” 50Sai ɗayansu ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama. 51Yesu ya amsa ya ce, “Ku ƙyale su haka.” Sai ya taɓa kunnen bawan, ya warkar da shi. 52Yesu kuma ya ce wa waɗanda suka tasar masa, wato, manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali da shugabannin jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake, kamar masu kama ɗan fashi? 53#Luk 19.47; 21.37 Sa'ad da nake tare da ku kowace rana a cikin Haikali, ba ku miƙa hannu garin ku kama ni ba. Amma wannan lokacinku ne da na ikon duhu.”
Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu
(Mat 26.57-58,69-75; Mar 14.53-54,66-72; Yah 18.12-18,25-27)
54Sai suka kama shi, suka tafi da shi, suka kai shi cikin gidan babban firist. Bitrus kuwa yana biye daga nesa nesa. 55Da suka hura wuta a tsakar gida suka zazzauna, Bitrus ma ya zauna a cikinsu. 56Sai wata baranya ta gan shi zaune a hasken wuta, ta zura masa ido, ta ce, “Ai, mutumin nan ma, tare da shi yake.” 57Amma ya musa ya ce, “Ke, ban ma san shi ba.” 58Bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, sai wani ya gan shi, ya ce, “Kai ma, ai, ɗayansu ne.” Amma Bitrus ya ce, “Ya mutum, ba haka ba ne.” 59Bayan wajen sa'a guda sai wani ya nace, ya ce, “Ba shakka mutumin nan ma tare da shi yake, don Bagalile ne.” 60Amma Bitrus ya ce, “Haba, ban ma san abin da kake faɗa ba.” Nan take, kafin ya rufe baki, sai zakara ya yi cara. 61Sai Ubangiji ya juya ya dubi Bitrus. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Ubangiji ya faɗa masa cewa, “A yau ma kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.” 62Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.
An Yi wa Yesu Ba'a, an Dūke Shi
(Mat 26.67-68; Mar 14.65)
63Sai mutanen da suke riƙe da Yesu suka yi ta masa ba'a, suna dūkansa. 64Suka ɗaure masa idanu, suka tambaye shi, suka ce, “Yi annabci! Wa ya buge ka?” 65Suka kuma yi ta masa baƙaƙen maganganu masu yawa, suna zaginsa.
Yesu a gaban 'Yan Majalisa
(Mat 26.59-66; Mar 14.55-64; Yah 18.19-24)
66Da gari ya waye sai majalisar shugabannin jama'a ta haɗu, da manyan firistoci da kuma malaman Attaura. Suka kai shi ɗakin majalisarsu suka ce, 67“To, in kai ne Almasihu, gaya mana.” Amma ya ce musu, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ba. 68In kuma na yi muku tambaya, ba za ku mai da jawabi ba. 69Amma nan gaba, Ɗan Mutum zai zauna dama na Allah Mai iko.” 70Duk suka ce, “Ashe, kai ɗin nan Ɗan Allah ne?” Sai ya ce musu, “Yadda kuka faɗa, ni ne.” 71Sai suka ce, “Wace shaida kuma za mu nema? Ai, mun ji da kanmu daga bakinsa.”

Zur Zeit ausgewählt:

Luk 22: HAU

Markierung

Teilen

Kopieren

None

Möchtest du deine gespeicherten Markierungen auf allen deinen Geräten sehen? Erstelle ein kostenloses Konto oder melde dich an.

YouVersion verwendet Cookies, um deine Erfahrung zu personalisieren. Durch die Nutzung unserer Webseite akzeptierst du unsere Verwendung von Cookies, wie in unserer Datenschutzrichtlinie beschrieben