Luk 21

21
Sadaka wadda aka Saka
(Mar 12.41-44)
1Yesu ya ɗaga kai ya ga waɗansu masu arziki suna saka sadakarsu a baitulmalin Haikali. 2Sai ya ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta saka rabin kobo biyu a ciki. 3Sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, abin da gajiyayyiya gwauruwan nan ta saka a ciki, ya fi na sauran duka. 4Domin duk waɗannan sun bayar daga yalwarsu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk kuɗinta na abinci.”
Yesu Ya Faɗi irin Rushewar da za ta Sami Haikali
(Mat 24.1-2; Mar 13.1-2)
5Waɗansu suna zancen Haikali, da yadda aka ƙawata shi da duwatsun alfarma da keɓaɓɓun kayan sadaka, sai ya ce, 6“In don waɗannan abubuwa da kuke kallo ne, ai, lokaci yana zuwa da ba wani dutsen da za a bari a nan a kan ɗan'uwansa da ba a baje shi ba.”
Alamu da Tsanance-tsanance
(Mat 24.3-14; Mar 13.3-13)
7Sai suka tambaye shi suka ce, “Malam, a yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa'ad da suke shirin aukuwa?” 8Sai ya ce, “Ku kula fa kada a ɓad da ku. Don mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, suna kuma cewa, ‘Lokaci ya yi kusa.’ To, kada ku bi su. 9In kuma kun ji labarin yaƙe-yaƙe da hargitsi, kada ku firgita. Lalle ne wannan ya fara aukuwa, amma ƙarshen tukuna.”
10Sa'an nan ya ce musu, “Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. 11Za a yi raurawar ƙasa manya manya, da kuma yunwa, da annoba a wurare dabam dabam. Za a kuma yi al'amura masu bantsoro da manyan alamu daga sama. 12Amma kafin wannan duka, za su kama ku, su tsananta muku. Za su miƙa ku ga majami'u da kurkuku, su kuma kai ku a gaban sarakuna da mahukunta saboda sunana. 13Wannan zai zama muku hanyar ba da shaida. 14#Luk 12.11,12 Saboda haka, sai ku ƙudura a ranku, a kan ba za ku damu da yadda za ku mai da jawabi ba. 15Domin ni ne zan ba ku ikon hurci, da kuma hikima wadda duk abokan adawarku, ba za su iya shanyewa ko musawa ba. 16Ko da iyayenku ma da 'yan'uwanku, da danginku, da abokanku, sai sun bāshe ku, su kuma sa a kashe waɗansunku. 17Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. 18Amma ba gashin kanku ko ɗaya da zai yi ciwo. 19Jurewarku ce za ta fisshe ku.”
Yesu ya Faɗi irin Ribɗewa da za ta Sami Urushalima
(Mat 24.15-28; Mar 13.14-23)
20“Sa'ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa'an nan ku tabbata ana kusan ribɗe ta. 21Sa'an nan waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, su gudu su shiga duwatsu, na birni su fice, na ƙauye kuma kada su shiga birni. 22#Yush 9.7 Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da yake rubuce. 23Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! Don matsanancin ƙunci zai saukar wa ƙasar, da kuma fushin Allah ga jama'an nan. 24Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al'ummai duka. Al'ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”
Komowar Ɗan Mutum
(Mat 24.29-31; Mar 13.24-27)
25 # Ish 13.10; Eze 32.7; Yow 2.31; W.Yah 6.12,13 “Za a kuma ga alamu a rana, da wata, da taurari, a duniya kuma al'ummai su matsu ƙwarai, suna shan damuwa saboda ƙugin teku da na raƙuman ruwa. 26Mutane za su suma don tsoro, da kuma fargaban al'amuran da suke aukuwa ga duniya, don za a girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama. 27#Dan 7.13; W.Yah 1.7 A sa'an nan ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare da iko da ɗaukaka mai yawa. 28Sa'ad da waɗannan al'amura suka fara aukuwa, sai ku ɗaga kai ku dubi sama, domin fansarku ta yi kusa.”
Aya a kan Itacen Ɓaure
(Mat 24.32-35; Mar 13.28-31)
29Sai ya ba su wani misali, ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa, 30da zarar sun fara toho, kuna gani, ku da kanku kun san damuna ta yi kusa ke nan. 31Haka kuma sa'ad da kuka ga waɗannan al'amura suna aukuwa, ku sani Mulkin Allah ya gabato. 32Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba, sai duk abubuwan nan sun auku. 33Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”
Gargaɗi a Zauna a Faɗake
34“Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko. 35Don haka, za ta auka wa mazaunan duniya duk, kowa da kowa. 36Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu'a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al'amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”
37 # Luk 19.47 Kullum da rana yakan koyar a Haikali, da dare kuma yakan fita ya kwana a dutsen da ake ce da shi Dutsen Zaitun. 38Da sassafe kuma dukan mutane sukan zo wurinsa a Haikali su saurare shi.

Zur Zeit ausgewählt:

Luk 21: HAU

Markierung

Teilen

Kopieren

None

Möchtest du deine gespeicherten Markierungen auf allen deinen Geräten sehen? Erstelle ein kostenloses Konto oder melde dich an.