YouVersion Logo
Search Icon

W.Yah 3

3
Saƙo Zuwa ga Sardisu
1“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Sardisu haka, ‘Ga maganar mai Ruhohin Allah guda bakwai, da kuma taurarin nan bakwai.
“ ‘Na san ayyukanka, kai rayayye ne, alhali kuwa matacce ne kai. 2Ka yi zaman tsaro, ka ƙarfafa abin nan da ya saura, yake kuma a bakin mutuwa, don ban ga aikinka cikakke ne ba a gaban Allahna. 3#Mat 24.43,44; Luk 12.39,40; W.Yah 16.15 Don haka, sai ka tuna da abin da ka karɓa ka kuma ji, ka kiyaye shi, sa'an nan ka tuba. In ba za ka yi tsaro ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san a lokacin da zan auko maka ba. 4Amma dai har yanzu kana da waɗansu kaɗan a Sardisu da ba su ƙazantar da kansu ba, za su kuwa kasance tare da ni da fararen kaya, don sun cancanta. 5#Fit 32.32,33; Zab 69.28; W.Yah 20.12; Mat 10.32; Luk 12.8 Duk wanda ya ci nasara, za a sa masa fararen tufafi, ba kuwa zan soke sunansa daga Littafin Rai ba, zan ce shi nawa ne a gaban Ubana, da kuma a gaban mala'ikunsa. 6Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”
Saƙo Zuwa ga Filadalfiya
7 # Ish 22.22; Ayu 12.14 “Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Filadalfiya haka, ‘Ga maganar Mai Tsarkin nan, Mai gaskiya, wanda yake da mabuɗin Dawuda, wanda in ya buɗe, ba mai rufewa, in kuma ya rufe, ba mai buɗewa.
8“ ‘Na san ayyukanka. Ka ga, na bar maka ƙofa a buɗe, wadda ba mai iya rufewa. Na dai san ƙarfinka kaɗan ne, duk da haka, kā kiyaye maganata, ba ka yi musun sanin sunana ba. 9#Ish 49.23; 60.14; Ish 43.4 To, ga shi, zan sa su waɗanda suke daga jama'ar Shaiɗan, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, ƙarya suke yi, zan sa su, su zo, su kwanta a gabanka, su sani dai na ƙaunace ka. 10Tun da yake ka kiyaye maganar da na yi maka ta yin jimiri, Ni ma zan kiyaye ka daga sharrin lokacin nan na gwaji, wanda zai auko wa dukan duniya, don a gwada mazaunan duniya. 11Ina zuwa da wuri. Ka riƙi abin da kake da shi kankan, kada wani ya karɓe maka kambinka. 12#W.Yah 21.2; Ish 62.2; 65.15 Duk wanda ya ci nasara, zan mai da shi ginshiƙi a Haikalin Allahna. Ba zai ƙara fita daga ciki ba, zan kuma rubuta sunan Allahna a jikinsa, da sunan Birnin Allahna, wato, Sabuwar Urushalima, mai saukowa daga wurin Allahna daga Sama, da kuma nawa sabon suna. 13Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”
Saƙo Zuwa ga Lawudikiya
14 # K.Mag 8.22 “Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Lawudikiya haka, ‘Ga maganar tabbataccen nan, Amintaccen Mashaidi mai gaskiya, wanda ta wurinsa dukkan halittar Allah ta kasance.
15“ ‘Na san ayyukanka. Ba ka da sanyi, ba ka kuwa da zafi. Da ma a ce kana da sanyi, ko kuwa kana da zafi. 16To, saboda kai tsakatsaki ne, ba ka da sanyi, ba ka kuwa da zafi, zan tofar da kai daga bakina. 17Tun da ka ce, kai mai arziki ne, cewa ka wadata ba ka bukatar kome, ba ka sani ba kuwa kai ne matsiyacin, abin yi wa kaito, matalauci, makaho, tsirara kuma. 18Saboda haka, ina yi maka shawara ka sayi zinariya a guna, wadda aka tace da wuta, don ka arzuta, da kuma fararen tufafi da za ka yi sutura, ka rufe tsiraicinka don kada ka ji kunya, da kuma man shafawa a ido don ka sami gani. 19#K.Mag 3.12; Ibr 12.6 Waɗanda nake ƙauna, su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka, sai ka himmantu ka tuba. 20Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni. 21Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin zama tare da ni a kursiyina. kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a kursiyinsa. 22Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”

Currently Selected:

W.Yah 3: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in