1
W.Yah 3:20
Littafi Mai Tsarki
Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni.
Compare
Explore W.Yah 3:20
2
W.Yah 3:15-16
“ ‘Na san ayyukanka. Ba ka da sanyi, ba ka kuwa da zafi. Da ma a ce kana da sanyi, ko kuwa kana da zafi. To, saboda kai tsakatsaki ne, ba ka da sanyi, ba ka kuwa da zafi, zan tofar da kai daga bakina.
Explore W.Yah 3:15-16
3
W.Yah 3:19
Waɗanda nake ƙauna, su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka, sai ka himmantu ka tuba.
Explore W.Yah 3:19
4
W.Yah 3:8
“ ‘Na san ayyukanka. Ka ga, na bar maka ƙofa a buɗe, wadda ba mai iya rufewa. Na dai san ƙarfinka kaɗan ne, duk da haka, kā kiyaye maganata, ba ka yi musun sanin sunana ba.
Explore W.Yah 3:8
5
W.Yah 3:21
Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin zama tare da ni a kursiyina. kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a kursiyinsa.
Explore W.Yah 3:21
6
W.Yah 3:17
Tun da ka ce, kai mai arziki ne, cewa ka wadata ba ka bukatar kome, ba ka sani ba kuwa kai ne matsiyacin, abin yi wa kaito, matalauci, makaho, tsirara kuma.
Explore W.Yah 3:17
7
W.Yah 3:10
Tun da yake ka kiyaye maganar da na yi maka ta yin jimiri, Ni ma zan kiyaye ka daga sharrin lokacin nan na gwaji, wanda zai auko wa dukan duniya, don a gwada mazaunan duniya.
Explore W.Yah 3:10
8
W.Yah 3:11
Ina zuwa da wuri. Ka riƙi abin da kake da shi kankan, kada wani ya karɓe maka kambinka.
Explore W.Yah 3:11
9
W.Yah 3:2
Ka yi zaman tsaro, ka ƙarfafa abin nan da ya saura, yake kuma a bakin mutuwa, don ban ga aikinka cikakke ne ba a gaban Allahna.
Explore W.Yah 3:2
Home
Bible
Plans
Videos