YouVersion Logo
Search Icon

Zab 28

28
Addu'ar Roƙo da Yabo
1Ina kira gare ka, ya Ubangiji mai kāre ni,
Ka ji kukana!
In kuwa ba ka amsa mini ba,
Zan zama ɗaya daga cikin waɗanda suka gangara zuwa lahira.
2Ka ji ni lokacin da na yi kuka gare ka neman taimako,
Ina ɗaga hannuwana wajen tsattsarkan Haikalinka.
3Kada ka kāshe ni tare da mugaye,
Tare da masu aikata mugunta,
Mutane waɗanda maganarsu kamar ta zumunci ce,
Amma zukatansu cike suke da ƙiyayya.
4 # W.Yah 22.12 Ka hukunta su saboda abin da suka aikata.
Ka hukunta su saboda dukan ayyukansu,
Ka ba su abin da ya cancance su!
5Ba su kula da abin da Ubangiji ya yi ba,
Ko kuma abin da ya halitta,
Don haka zai hukunta su, ya hallaka su har abada.
6A yabi Ubangiji,
Gama ya ji kukana na neman taimako!
7Ubangiji yakan kiyaye ni, yă tsare ni.
Na dogara gare shi.
Ya taimake ni, don haka ina murna,
Ina raira masa waƙoƙin yabo.
8Ubangiji yana kiyaye jama'arsa,
Yakan kiyaye sarkinsa da ya zaɓa, ya kuma cece shi.
9Ka ceci jama'arka, ya Ubangiji,
Ka sa wa waɗanda suke naka albarka!
Ka zama makiyayinsu,
Ka lura da su har abada.

Currently Selected:

Zab 28: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in