Zab 27
27
Ubangiji Ne Haskena da Cetona
1Ubangiji ne haskena da cetona,
Ba zan ji tsoron kowa ba.
Ubangiji yana kiyaye ni daga dukan hatsari,
Ba zan ji tsoro ba.
2Sa'ad da mugaye suka tasar mini,
Suna ƙoƙari su kashe ni,
Za su yi tuntuɓe su fāɗi.
3Ko da rundunar mayaƙa ta kewaye ni,
Ba zan ji tsoro ba.
Ko da magabtana sun tasar mini,
Zan dogara ga Allah.
4Abu guda nake roƙo a wurin Ubangiji,
Abu ɗaya kaɗai nake bukata,
Shi ne in zauna a masujadar Ubangiji,
In yi ta al'ajabin alherinsa
Dukan kwanakin raina,
In roƙi biyarwarsa a can.
5A lokatan wahala zai kiyaye ni a inuwarsa,
Zai kiyaye ni lafiya a Haikalinsa,
Zai ɗora ni a kan dutse mai tsayi, ya kiyaye ni.
6Ta haka zan ci nasara a kan magabtana da suke kewaye da ni.
Da sowar farin ciki mai yawa zan miƙa sadakoki a Haikalinsa!
Zan raira waƙa, in yabi Ubangiji!
7Ka ji ni, ya Ubangiji, sa'ad da na ya yi kira gare ka!
Ka yi mini jinƙai ka amsa mini!
8Ka ce, “Zo wurina,”
Zan kuwa zo gare ka, ya Ubangiji,
9Kada ka ɓoye mini fuskarka, ya Ubangiji!
Kada ka yi fushi da ni,
Kada kuwa ka kori bawanka.
Kai ne kake taimakona, tun dā ma,
Kada ka bar ni, kada ka yashe ni,
Ya Allahna, Mai Cetona!
10Mai yiwuwa ne ubana da uwata su yashe ni,
Amma Ubangiji zai lura da ni.
11Ka koya mini abin da ya kamata in yi, ya Ubangiji,
Ka bi da ni kan lafiyyiyar hanya,
Domin ina da magabta da yawa.
12Kada ka bar ni a hannun magabtana,
Waɗanda suke fāɗa mini da ƙarairayi da kurari.
13Hakika zan rayu domin in ga alherin Ubangiji
Da zai yi wa jama'arsa.
14Ka dogara ga Ubangiji!
Ka yi imani, kada ka karai.
Ka dogara ga Ubangiji!
Currently Selected:
Zab 27: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979