YouVersion Logo
Search Icon

Mika 5

5
1Ki tattara sojojinki, gama an
kewaye mu da yaƙi.
Za su bugi kumatun Sarkin Isra'ila
da sanda.
Mulkin Mai Ceto daga Baitalami
2 # Mat 2.6; Yah 7.42 “Baitalami cikin Efrata,
Wadda kike 'yar ƙarama a cikin
kabilar Yahuza,
Amma daga cikinki wani zai fito
wanda zai sarauci Isra'ila
Wanda asalinsa tun fil azal ne.”
3Domin haka zai yashe su,
Sai lokacin da wadda take naƙuda ta
haihu.
Sa'an nan sauran 'yan'uwansa
Za su komo wurin mutanen Isra'ila.
4Shi kuwa zai tashi ya ciyar da
garkensa da ƙarfin Ubangiji,
Da ɗaukakar sunan Ubangiji
Allahnsa.
Za su kuwa zauna lafiya,
Gama zai zama mai girma cikin
duniya duka.
5Zai zama salamarmu.
Ceto da Hukunci
Sa'ad da kuma Assuriyawa za su
kawo mana yaƙi,
Za su tattake kagaranmu,
Za mu sa makiyaya bakwai da
shugabanni takwas su yi gāba da
su.
6 # Far 10.8-11 Za su mallaki ƙasar Assuriya da
takobi,
Su shiga ƙofofin ƙasar Nimrod da
zararren takobi,
Zai cece mu daga hannun
Ba'assuriye,
Sa'ad da ya kawo wa ƙasarmu
yaƙi,
Sa'ad da kuma ya tattake ƙasarmu.
7Sa'an nan ringin Yakubu zai zamar
wa mutane
Kamar raɓa daga wurin Ubangiji,
Kamar kuma yayyafi a kan tsire-tsire,
Wanda ba ya jinkiri ko ya jira
mutane.
8Ringin Yakubu kuma zai zamar wa
al'umman duniya,
Kamar yadda zaki yake a tsakanin
namomin jeji,
Kamar kuma yadda zaki yake a
tsakanin garkunan tumaki,
Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakan
tattaka,
Ya yi kacakaca da su,
Ba wanda zai cece su.
9Za a ƙarfafa hannunka a kan
maƙiyanka,
Za a datse maƙiyanka duka.
10“A wannan rana, ni Ubangiji na ce,
Zan kashe dawakanku, in hallaka
karusanku.
11Zan shafe biranen ƙasarku,
In rushe garunku.
12Zan kawar da maita daga ƙasarku,
Ba za ku ƙara samun bokaye ba.
13Zan sassare siffofinku da
ginshiƙanku,
Ba za ku ƙara sunkuya wa aikin
hannuwanku ba.
14Zan tumɓuke gumakan nan Ashtarot
daga cikinku,
Zan hallaka biranenku.
15Da fushi da hasala zan yi sakayya
A kan al'umman da ba su yi biyayya
ba.”

Currently Selected:

Mika 5: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in