YouVersion Logo
Search Icon

Mika 6

6
Ubangiji Yana Gāba da Isra'ila
1“Ku ji abin da ni Ubangiji nake cewa,
Tashi ku gabatar da ƙararku a
gaban duwatsu,
Ku bar tuddai su ji muryarku.
2“Ku duwatsu da madawwaman tussan duniya,
Ku ji tuhumar da Ubangiji yake yi muku.
Gama Ubangiji, yana da magana
gāba da mutanensa,
Zai tuhumi Isra'ila.
3“Ya ku jama'ata, me na yi muku?
Wace irin fitina nake yi muku?
Ku amsa mini!
4 # Fit 12.50,51; Fit 4.10-16; Fit 15.20 Gama na fito da ku daga ƙasar Masar,
Na fanshe ku daga gidan bauta.
Na aika muku da Musa, da Haruna,
da Maryamu.
5 # L.Ƙid 22.2—24.25; Josh 3.1—4.19 Ya ku jama'ata, ku tuna
Da abin da Balak, Sarkin Mowab, ya ƙulla,
Da yadda Bal'amu ɗan Beyor ya
amsa masa,
Da abin da ya faru daga Shittim, har
zuwa Gilgal,
Don ku san ayyukan adalci na Ubangiji.”
Abin da Allah Yake So ga Mutane
6Da me zan zo gaban Ubangiji,
In sunkuyar da kaina a gaban Allah na Sama?
Ko in zo gabansa da maraƙi bana
ɗaya domin yin hadaya ta ƙonawa?
7Ubangiji zai yi murna da raguna dubbai
Ko kuwa da kogunan mai dubbai?
Zan ba da ɗan farina ne don
laifina?
Ko kuwa zan ba da 'ya'yana saboda zunubina?
8Ya kai mutum, ya riga ya nuna
maka abin da yake mai kyau.
Abin da Ubangiji yake so gare ka,
shi ne
Ka yi adalci, ka ƙaunaci aikata alheri,
Ka bi Allah da tawali'u.
9Ubangiji yana kira ga birnin.
Hikima ce ƙwarai a ji tsoron sunanka.
“Ki ji ya kabila, wa ya sa miki
lokacinki?
10Ba zan manta da dukiya ta mugunta
a gidan mugu ba,
Ba kuwa zan manta da bugaggen
mudun awo ba.
11Zan kuɓutar da mutum mai ma'auni
na cuta
Da ma'aunin ƙarya?
12Attajiran birnin sun cika zalunci,
Mazaunansa kuwa maƙaryata ne,
Harshensu na yaudara ne.
13Domin haka zan buge ku da ciwo,
In maishe ku kufai saboda zunubanka.
14Za ka ci, amma ba za ku ƙoshi ba,
Yunwa za ta kasance a cikinku,
Za ku tanada, amma ba zai tanadu ba,
Abin da kuma kuka tanada zan bai
wa takobi.
15Za ku shuka, amma ba za ku girbe ba.
Za ku matse 'ya'yan zaitun, amma
ba za ku shafa mansa ba,
Za ku kuma matse 'ya'yan inabi,
amma ba za ku sha ruwansa ba.
16 # 1Sar 16.23-28; 1Sar 16.29-34; 21.25,26 Domin kun kiyaye dokokin Omri,
Kun bi halin gidan Ahab,
Kun kuma bi shawarwarinsu.
Domin haka zan maishe ku kufai,
In mai da ku abin dariya,
Za ku sha raini a wurin mutanena.”

Currently Selected:

Mika 6: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in