YouVersion Logo
Search Icon

Mat 9

9
Yesu Ya Warkar da Shanyayye
(Mar 2.1-12; Luk 5.17-26)
1Da ya shiga jirgi, ya haye ya je garinsu. 2Sai aka kawo masa wani shanyayye, kwance a gado. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, ka yi farin ciki, an gafarta maka zunubanka.” 3Sai waɗansu malaman Attaura suka ce a ransu, “Wannan mutum, ai, saɓo yake!” 4Yesu kuwa, da yake ya san tunaninsu, ya ce, “Don me kuke mugun tunani a zuciyarku? 5Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya’? 6Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya” sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.” 7Shi kuwa ya tashi ya tafi gida. 8Da taron suka ga haka, sai tsoro ya kama su, suka ɗaukaka Allah, wanda ya ba mutane iko haka.
Kiran Matiyu
(Mar 2.13-17; Luk 5.27-32)
9Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.
10 # Luk 15.1,2 Sa'ad da kuwa Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa. 11Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 12Amma da Yesu ya ji haka ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. 13#Mat 12.7; Yush 6.6 Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba.’ Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi.”
Tambaya a kan Azumi
(Mar 2.18-22; Luk 5.33-39)
14Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, “Don me mu da Farisiyawa mukan yi azumi, amma naka almajiran ba sa yi?” 15Sai Yesu ya ce musu, “Abokan ango sa yi baƙin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi. 16Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle, don mahon zai kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa. 17Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai salkunan su fashe, ruwan inabin ya zube, salkunan kuma su lalace. Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna. Ta haka an tserar da duka biyu ke nan.”
'Yar Shugaban Jama'a da Matar da ta Taɓa Gezar Mayafin Yesu
(Mar 5.21-43; Luk 8.40-56)
18Yana cikin yi musu magana haka, sai ga wani shugaban jama'a ya zo, ya yi masa sujada, ya ce, “Yanzu yanzu 'yata ta rasu, amma ka zo ka ɗora mata hannu, za ta rayu.” 19Sai Yesu ya tashi, ya bi shi tare da almajiransa. 20Ga kuma wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa, 21domin ta ce a ranta, “Ko da mayafinsa ma na taɓa, sai in warke.” 22Sai Yesu ya juya, yă gan ta, ya ce, “'Yata, ki yi farin ciki, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take matar ta warke.
23Da Yesu ya isa gidan shugaban jama'ar, ya kuma ga masu busar sarewa da taro suna ta hayaniya, 24sai ya ce, “Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci take yi.” Sai suka yi masa dariyar raini. 25Amma da aka fitar da taron waje, ya shiga ya kama hannunta, sai kuwa yarinyar ta tashi. 26Wannan labarin kuwa ya bazu a duk ƙasar.
Makafi Biyu Sun Sami Ganin Gari
27Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna ɗaga murya suna cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu.” 28Da ya shiga wani gida sai makafin suka zo gare shi. Yesu ya ce musu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?” Sai suka ce masa, “I, ya Ubangiji!” 29Sa'an nan ya taɓa idanunsu, ya ce, “Yă zama muku gwargwadon bangaskiyarku.” 30Sai idanunsu suka buɗe. Amma Yesu ya kwaɓe su ƙwarai, ya ce, “Kada fa kowa ya ji labarin.” 31Amma suka tafi suka yi ta baza labarinsa a duk ƙasar.
Bebe Ya Yi Magana
32Sun tashi ke nan, sai aka kawo masa wani bebe mai aljan. 33Bayan an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, suka ce, “Kai! Ba a taɓa ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba.” 34#Mat 10.25; 12.24; Mar 3.22; Luk 11.15 Amma sai Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”
Yesu Ya Ji Tausayin Mutane
35 # Mat 4.23; Mar 1.39; Luk 4.44 Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. 36#L.Ƙid 27.17; 1Sar 22.17; 2Tar 18.16; Eze 34.5; Mar 6.34 Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala, suna nan a warwatse kamar tumaki da ba makiyayi. 37#Luk 10.2 Sai ya ce wa almajiransa, “Girbin yana da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. 38Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbin ya turo masu girbi, su yi masa girbi.”

Currently Selected:

Mat 9: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in