YouVersion Logo
Search Icon

Mat 8

8
Yesu Ya Warkar da Kuturu
(Mar 1.40-45; Luk 5.12-16)
1Da ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawan gaske suka bi shi. 2Sai ga wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.” 3Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take kuturtarsa ta warke. 4#L.Fir 14.1-32 Sai Yesu ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”
Yesu Ya Warkar da Yaron Wani Jarumi
(Luk 7.1-10)
5Yana shiga Kafarnahum ke nan, sai wani jarumi ya zo gunsa ya roƙe shi, 6ya ce, “Ya Ubangiji, yarona na kwance a gida, ya zama shanyayye, yana shan azaba ƙwarai.” 7Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.” 8Sai jarumin, ya ce, “Ya Ubangiji, ban isa har ka zo gidana ba, amma sai ka yi magana kawai, yarona kuwa zai warke. 9Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, sai in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.” 10Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba. 11#Luk 13.29 Ina kuma gaya muku, da yawa za su zo daga gabas da yamma su zauna cin abinci tare da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a Mulkin Sama, 12#Mat 22.13; 25.30; Luk 13.28 'ya'yan Mulki kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.” 13Sai Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka, ya zama maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi.” Nan take yaronsa ya warke.
Yesu Ya Warkar da Surukar Bitrus
(Mar 1.29-31; Luk 4.38-39)
14Da Yesu ya shiga gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzaɓi. 15Sai ya taɓa hannunta, zazzaɓin ya sake ta, ta kuma tashi ta yi masa hidima.
Yesu Ya Warkar da Mutane da Yawa da Maraice
(Mar 1.32-34; Luk 4.40-41)
16Da maraice ya yi, sai suka kakkawo masa masu aljannu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljannun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. 17#Ish 53.4 Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa, “Da kansa ya ɗebe rashin lafiyarmu, ya ɗauke cucecucenmu.”
Masu Cewa, Za Su Bi Yesu
(Luk 9.57-62)
18To, da Yesu ya ga taro masu yawan gaske sun kewaye shi, sai ya yi umarni a koma wancan hayi. 19Sai wani malamin Attaura ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.” 20Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da sheƙunan, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.” 21Sai ɗaya daga almajiran ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.” 22Amma Yesu ya ce masa, “Bi ni. Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu.”
Yesu Ya Tsawata wa Hadiri
(Mar 4.35-41; Luk 8.22-25)
23Da ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi. 24Sai ga wani babban hadiri ya taso a teku, har raƙuman ruwa suka fara shan kan jirgin, amma yana barci. 25Sai almajiransa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ya Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!” 26Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa'an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit! 27Mutanen suka yi al'ajabi, suka ce, “Wane irin mutum ne wannan, wanda har iska da ruwan teku ma suke masa biyayya?”
Warkar da Masu Aljannu na Garasinawa
(Mar 5.1-20; Luk 8.26-39)
28Da ya isa wancan hayi a ƙasar Garasinawa, mutum biyu masu aljannu suka fito daga makabarta suka tarye shi. Don kuwa su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bi ta wannan hanya. 29Sai suka ƙwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?” 30Nesa kuma kaɗan akwai wani babban garken alade na kiwo. 31Sai aljannun suka roƙe shi, suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladen nan.” 32Ya ce musu, “To, ku je.” Sai suka fita, suka shiga aladen. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka faɗa tekun, suka hallaka a ruwa. 33Masu kiwon aladen suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin kome da kome, da kuma abin da ya auku ga masu aljannun. 34Sai ga duk jama'ar garin sun firfito su taryi Yesu. Da suka gan shi, sai suka roƙe shi ya bar musu ƙasarsu.

Currently Selected:

Mat 8: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in