YouVersion Logo
Search Icon

Mat 2

2
Ziyarar Masana Taurari daga Gabas
1Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa, 2“Ina wanda aka haifa Sarkin Yahudawa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo mu yi masa sujada.” 3Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima. 4Sai ya tara dukan manyan firistoci da malaman Attaura na jama'a, ya tambaye su inda za a haifi Almasihu. 5Sai suka ce masa, “A Baitalami ne, ta ƙasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta cewa,
6 # Mika 5.2 “ ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza,
Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba,
Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki,
Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.’ ”
7Sai Hirudus ya kira masanan nan a asirce, ya tabbata daga bakinsu ainihin lokacin da tauraron nan ya bayyana. 8Sa'an nan ya aike su Baitalami, ya ce, “Ku je ku binciko mini ɗan yaron nan sosai. In kun same shi, ku kawo mini labari, don ni ma in je in yi masa sujada.” 9Su kuwa da suka ji maganar sarki, sai suka yi tafiyarsu. Ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gabansu, har ya zo ya tsaya bisa inda ɗan yaron nan yake. 10Da suka ga tauraron sai suka yi matuƙar farin ciki. 11Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron, tare da uwa tasa Maryamu, suka fāɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwar zinariya, da lubban, da mur. 12Amma da aka gargaɗe su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.
Gudu zuwa Masar
13Da suka tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu ƙasar Masar, ka zauna a can sai na faɗa maka, don Hirudus yana shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi.” 14Yusufu kuwa ya tashi ya ɗauki ɗan yaron da uwa tasa da daddare, ya tafi Masar, 15#Yush 11.1 ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya faɗa ne ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kirawo Ɗana.”
Kisan 'Yan Yara
16Da Hirudus ya ga masanan nan sun mai da shi wawa, sai ya hasala ƙwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan nan. 17A lokacin ne aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa,
18 # Irm 31.15 “An ji wata murya a Rama,
Ta kuka da baƙin ciki mai zafi,
Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta.
Ba za ta ta'azantu ba, don ba su.”
Komowa daga Masar
19Amma bayan mutuwar Hirudus, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar, ya ce, 20“Tashi ka ɗauki ɗan yaron da uwa tasa, ka tafi ƙasar Isra'ila, don masu neman ran ɗan yaron sun mutu.” 21Sai ya tashi, ya ɗauki ɗan yaron da uwa tasa, ya zo ƙasar Isra'ila. 22Amma da ya ji Arkilayus ya gāji ubansa Hirudus, yana mulkin ƙasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Amma da aka yi masa gargaɗi a mafarki, sai ya ratse zuwa ƙasar Galili. 23#Mar 1.24; Luk 2.39; Yah 1.45 Sai ya je ya zauna a wani gari wai shi Nazarat, domin a cika faɗar annabawa cewa, “Za a kira shi Banazare.”

Currently Selected:

Mat 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in