YouVersion Logo
Search Icon

Mat 18

18
Wane ne Mafi Girma?
(Mar 9.33-37; Luk 9.46-48)
1 # Luk 22.24 A lokacin nan almajirai suka zo wurin Yesu, suka ce, “Wa ya fi girma duka a Mulkin Sama?” 2Sai ya kira wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu, 3#Mar 10.15; Luk 18.17 ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in ba kun juyo kun zama kamar ƙananan yara ba, har abada ba za ku shiga Mulkin Sama ba. 4Duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar ɗan yaron nan, ai, shi ne mafi girma a Mulkin Sama.
5“Wanda duk ya karɓi ƙaramin yaro ɗaya kamar wannan saboda sunana, Ni ya karɓa. 6Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.”
Sanadodin Yin Zunubi
(Mar 9.42-48; Luk 17.1-2)
7“Kaiton duniya saboda sanadodin tuntuɓe! Lalle sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadin! 8#Mat 5.30 In kuwa hannunka ko ƙafarka suna sa ka laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai dungu ko da gurguntaka, da a jefa ka madawwamiyar wuta da hannu biyu ko ƙafa biyu. 9#Mat 5.29 In kuwa idonka yana sa ka laifi, to ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da a jefa ka Gidan Wuta da ido biyu.”
Misali na Ɓatacciyar Tunkiya
(Luk 15.3-7)
10 # Luk 19.10 “Ku dai lura, kada ku raina ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara. Ina gaya muku, mala'ikunsu a Sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin Sama. 11[Domin Ɗan Mutum ya zo ne musamman ceton abin da ya ɓata.] 12To, me kuka gani? In wani na da tumaki ɗari, ɗayarsu ta băce, ashe, ba zai bar tasa'in da taran nan a gindin dutse, ya je neman wadda ta ɓăce ba? 13In kuwa ya samo ta, labudda, ina gaya muku, ai, farin cikin da yake yi a kanta ya fi na tasa'in da taran nan da ba su taɓa ɓăcewa ba. 14Haka ma, ba nufin Ubanku da yake cikin Sama ba ne ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya hallaka.”
Ɗan'uwan da Ya Yi Laifi
(Luk 17.3)
15 # Luk 17.3 “In ɗan'uwanka ya yi maka laifi, sai ka je, ka gaya masa laifinsa, kai da shi, ku kaɗai. In ya saurare ka, to, kā maido da ɗan'uwanka ke nan. 16#M.Sh 19.15 In kuwa bai saurare ka ba, sai ka tafi da mutum ɗaya ko biyu, don a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku. 17In kuma ya ƙi sauraronsu, sai ka shaida wa ikilisiya. In kuma har ya ƙi sauraron ikilisiyar, ka maishe shi kamar bare, ko mai karɓar haraji.”
Kullewa da Warwarewa
18 # Mat 16.19; Yah 20.23 “Hakika, ina gaya muku, kome kuka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome kuka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne. 19Har wa yau dai ina gaya muku, in mutum biyu daga cikinku, ra'ayinsu ya zo ɗaya a nan duniya a kan wani abin da za su roƙa, Ubana kuwa da yake Sama zai yi musu shi. 20Gama kuwa inda mutum biyu ko uku suka taru saboda sunana, ni ma ina nan a tsakiyarsu.”
Misali na Bawa Wanda Bai Yafe Ba
21 # Luk 17.3,4 Sai Bitrus ya matso ya ce masa, “Ya Ubangiji, sau nawa ɗan'uwana zai yi mini laifi in yafe masa? Har sau bakwai?” 22#Far 4.24 Yesu ya ce masa, “Ba sau bakwai kawai na ce maka ba, sai dai bakwai har saba'in.
23“Saboda haka za a misalta Mulkin Sama da wani sarkin da yake so ya yi ƙididdigar dukiyarsa da yake hannun bayinsa. 24Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wanda yake bi talanti dubu goma bashi. 25Da yake ya gagara biya, sai ubangidansa ya yi umarni a sayar da shi da mata tasa da 'ya'yansa da kuma duk abin da ya mallaka, a biya kuɗin. 26Sai bawan ya faɗi a gabansa ya yi masa ladabi, ya ce, ‘Ya ubangida, ka yi mini haƙuri, zan biya ka tsaf.’ 27Saboda tausayin bawan nan ubangidansa ya sake shi, ya yafe masa bashin. 28Amma wannan bawa, da fitarsa sai ya tarar da wani abokin bautarsa, wanda yake bi dinari ɗari bashi. Ya cafi wuyarsa, ya ce, ‘Biya ni abin da nake binka.’ 29Sai abokin bautarsa ya faɗi a gabansa, ya yi ta roƙonsa ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, ai, zan biya ka.’ 30Amma ya ƙi, ya kuma je ya sa shi a kurkuku, har yā biya bashin. 31Da abokan bautarsa suka ga abin da ya faru, suka yi baƙin ciki gaya, har suka je suka gaya wa ubangidansu duk abin da ya gudana. 32Sai ubangiji nasa ya kira shi, ya ce masa, ‘Kai mugun bawa ne! Na yafe maka duk bashin nan saboda ka roƙe ni, 33ashe, bai kyautu kai ma ka ji tausayin abokin bautarka, kamar yadda na ji tausayinka ba?’ 34Ubangijinsa ya yi fushi, ya ba da shi ga masu azabtarwa har yă biya duk bashin da ake binsa. 35Haka kuma Ubana da yake Sama zai yi da ko wannenku, in ba ku yafe wa 'yan'uwanku da zuciya ɗaya ba.”

Currently Selected:

Mat 18: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in