YouVersion Logo
Search Icon

Mat 17

17
Sākewar Kamanninsa
(Mar 9.2-13; Luk 9.28-36)
1Bayan kwana shida sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da ɗan'uwansa Yahaya, ya kai su a kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. 2Sai kamanninsa suka sāke a gabansu, fuskarsa ta yi annuri kamar hasken rana, tufafinsa kuma suka yi fari fat suna haske. 3Ga shi, Musa da Iliya sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu. 4Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin. In kana so, sai in kafa bukkoki uku a nan, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” 5#Far 22.2; Zab 2.7; Ish 42.1; Mat 3.17; 12.18; Mar 1.11; Luk 3.22; M.Sh 18.15#2Bit 1.17,18 Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.” 6Da almajiran suka ji haka, sai suka faɗi ƙasa, tsoro ya kama su. 7Sai Yesu ya zo ya taɓa su, ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” 8Da suka ɗaga kai ba su ga kowa ba, sai Yesu kaɗai.
9Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.” 10#Mal 4.5Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, yaya malaman Attaura suke cewa, lalle ne Iliya ya riga zuwa?” 11Ya amsa ya ce, “Lalle Iliya zai zo ne, zai kuwa raya dukan abubuwa. 12#Mat 11.14 Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa san shi ne ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗan Mutum zai sha wuya a hannunsu.” 13Sa'an nan ne almajiran suka gane, ashe, zancen Yahaya Maibaftisma yake yi musu.
Yesu Ya Warkar da Yaro Mai Beben Aljan
(Mar 9.14-29; Luk 9.37-43)
14Da suka isa wurin taro, sai wani mutum ya zo gare shi, ya durƙusa a gabansa, ya ce, 15“Ya Ubangiji, ka ji tausayin ɗana, yana farfaɗiya, yana shan wuya ƙwarai, sau da yawa yakan faɗa wuta da kuma ruwa. 16Na kuwa kai shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.” 17Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.” 18Sai Yesu ya tsawata masa, aljanin kuma ya rabu da shi. Nan take yaron ya warke. 19Sa'an nan almajiran suka zo wurin Yesu a keɓe, suka ce, “Me ya sa mu muka kasa fitar da shi?” 20#Mat 21.21; Mar 11.23; 1Kor 13.2 Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, ‘Kawu daga nan, ka koma can!’, sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku. 21[Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a da azumi.]”
Yesu Ya Sāke Faɗar Irin Mutuwar da Zai Yi
(Mar 9.30-32; Luk 9.43-45)
22Tun suna ƙasar Galili, sai Yesu ya ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane, 23za su kuwa kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Sai duk tsananin baƙin ciki ya rufe su.
Ba Da Gudunmawar Haikali
24 # Fit 30.13; 38.26 Da suka zo Kafarnahum masu karɓar rabin shekel na gudunmawar Haikali suka je wurin Bitrus, suka ce, “Malaminku yana ba da gudunmawar?” 25Ya ce, “I, yakan bayar.” Da ya dawo gida kuma, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani, Bitrus? Wurin wa sarakunan duniya suke karɓar kuɗin fito ko haraji, a wurin 'ya'yansu, ko kuwa daga wurin waɗansu?” 26Sa'ad da kuma ya ce, “Daga wurin waɗansu,” sai Yesu ya ce masa, “Wato, 'ya'yan an ɗauke musu ke nan. 27Duk da haka, don kada mu ba su haushi, ka je teku ka yi fatsa, kifin da ka fara kamawa kuwa shi za ka ɗauka. In ka buɗe bakinsa za ka sami shekel guda a ciki. To, sai ka ɗauki shekel ɗin nan ka kai musu, wato, nawa da naka.”

Currently Selected:

Mat 17: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in