YouVersion Logo
Search Icon

Mat 12

12
Almajirai Na Zagar Alkama Ran Asabar
(Mar 2.23-28; Luk 6.1-5)
1 # M.Sh 23.25 A lokacin nan a ran Asabar, Yesu yana ratsa gonakin alkama. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara zagar alkamar suna ci. 2Amma da Farisiyawa suka ga haka, suka ce masa, “Ka ga! Almajiranka suna yin abin da bai halatta a yi ran Asabar ba.” 3#1Sam 21.1-6 Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa'ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa? 4#L.Fir 24.9 Yadda ya shiga Ɗakin Allah ya ci keɓaɓɓiyar gurasar nan, wadda bai halatta ya ci ba, ko abokan tafiyarsa ma su ci ba, sai dai firistoci kaɗai? 5#L.Ƙid 28.9,10 Ko kuwa ba ku taɓa karantawa a Attaura ba, yadda a ran Asabar, firistoci a Haikalin sukan keta dokar Asabar, ba tare da yin wani laifi ba kuwa? 6Ina dai gaya muku, ga wanda ya fi Haikali a nan. 7#Mat 9.13; Yush 6.6 Da kun san ma'anar wannan cewa, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba’, da ba ku ga laifin marasa laifi ba. 8Domin Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”
Mai Shanyayyen Hannu
(Mar 3.1-6; Luk 6.6-11)
9Sai ya ci gaba daga nan ya shiga majami'arsu. 10Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. Sai suka tambayi Yesu, suka ce, “Ya halatta a warkar a ran Asabar?” Wannan kuwa don su samu su kai ƙararsa ne. 11#Luk 14.5 Ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da tunkiya, ta faɗa a rami ran Asabar, ba zai kama ta ya fitar da ita ba? 12Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja? Domin haka ya halatta a yi alheri a ran Asabar.” 13Sa'an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa. Sai ya koma lafiyayye kamar ɗayan. 14Amma Farisiyawa suka fita, suka yi shawara a kansa, yadda za su hallaka shi.
Zaɓaɓɓen Bara
15Da Yesu ya gane haka, ya tashi daga nan. Sai jama'a da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su duka. 16Sai ya kwaɓe su, kada su bayyana shi. 17Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,
18 # Ish 42.1-4 “Ga barana wanda na zaɓa!
Ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai.
Zan sa masa Ruhuna, zai kuma sanar da al'ummai hanyar gaskiya.
19Ba zai yi husuma ko magana sama sama ba,
Ba kuma wanda zai ji muryarsa tasa a titi.
20Kyauron da ya tanƙwasa ba zai kakkarye shi ba,
Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba,
Har ya sa gaskiya ta ci nasara.
21Al'ummai kuma za su sa zuciya ga sunansa.”
Yesu da Ba'alzabul
(Mar 3.19-30; Luk 11.14-23)
22Sai aka kawo masa wani beben makaho mai aljan, ya kuwa warkar da shi, har beben ya yi magana, ya kuma gani. 23Mutane duk suka yi al'ajabi, suka ce, “Shin, ko wannan shi ne Ɗan Dawuda?” 24#Mat 9.34; 10.25 Amma da Farisiyawa suka ji haka sai suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu kawai, wannan yake fitar da aljannu.” 25Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Ba kuma gari ko gidan da ya rabu a kan gāba, yă ɗore. 26In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, yā rabu a kan gāba ke nan. To, ta yaya mulkinsa zai ɗore? 27In kuwa da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu, to, 'ya'yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka su ne za su zama alƙalanku. 28Ni kuwa in da ikon Ruhun Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan. 29Yaya za a iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum a washe kayansa, in ba an fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin ba? Sa'an nan ne za a iya washe gidansa. 30#Mar 9.40 Wanda ba nawa ba ne, gāba yake da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.
31“Don haka ina gaya muku, ā gafarta wa mutane kowane zunubi da saɓo, amma wanda ya saɓi Ruhun, ba za a gafarta masa ba. 32#Luk 12.10 Kowa ya aibata Ɗan Mutum, ā gafarta masa. Amma wanda ya aibata Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, duniya da lahira.”
Itace da 'Ya'yansa
(Luk 6.43-45)
33 # Mat 7.20; Luk 6.44 “Ko dai ku ce itace kyakkyawa ne, 'ya'yansa kuma kyawawa, ko kuwa ku ce itace mummuna ne, 'ya'yansa kuma munana. Don itace, da 'ya'yansa ake gane shi. 34#Mat 3.7; 23.33; Luk 3.7; Mat 15.18; Luk 6.45 Ku macizai! Yaya za ku iya yin maganar kirki, alhali kuwa ku mugaye ne? Don abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa. 35Mutumin kirki kam, ta kyakkyawar taskar zuciya tasa yakan yi abin kirki, mugu kuwa, ta mummunar taskar zuciya tasa yakan yi mugun abu. 36Ina dai gaya muku, a Ranar Shari'a duk hululun da mutum ya yi, za a bincike shi. 37Maganarka ce za ta kuɓutar da kai, ko kuma ta hukunta ka.”
'Yan Zamani Suna Neman Alama
(Mar 8.12; Luk 11.29-32)
38 # Mat 16.1; Mar 8.11; Luk 11.16 Waɗansu malaman Attaura da Farisiyawa suka amsa masa suka ce, “Malam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.” 39#Mat 16.4; Mar 8.12 Sai ya amsa musu ya ce, “'Yan zamani, mugaye, maciya amana, suke nema su ga wata alama! Amma ba wata alama da za a nuna musu sai dai ta Annabi Yunusa. 40#Yun 1.17 Wato, kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗan Mutum zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa. 41#Yun 3.5 A Ranar Shari'a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su kā da su, don sun tuba saboda wa'azin Yunusa. Ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan. 42#1Sar 10.1-10; 2Tar 9.1-12 A Ranar Shari'a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan, ta kā da su, don ta zo ne daga bangon duniya ta ji hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan.
Komawar Baƙin Aljan
(Luk 11.24-26)
43“Baƙin aljan in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa neman hutu, amma ba ya samu. 44Sa'an nan sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’ Sa'ad da kuwa ya koma, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, ƙawatacce. 45Daga nan ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa. Haka zai zamar wa wannan mugun zamani.”
Uwar Yesu da 'Yan'uwansa
(Mar 3.31-35; Luk 8.19-21)
46Yana cikin magana da taro, sai ga Uwa tasa da 'yan'uwansa suna tsaye a waje, suna nema su yi magana da shi. 47Wani ya ce masa, “Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.” 48Sai ya amsa wa wanda ya gaya masa, ya ce, “Wace ce tsohuwata, su wane ne kuma 'yan'uwana?” 49Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa, ya ce, “Ga nan tsohuwata da 'yan'uwana nan! 50Ai, kowa ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so, shi ne ɗan'uwana, shi ne 'yar'uwata, shi ne kuma tsohuwata.”

Currently Selected:

Mat 12: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in