YouVersion Logo
Search Icon

Mat 10

10
Yesu Ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu
(Mar 3.13-19; Luk 6.12-16)
1Sai ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da baƙaƙen aljannu, su warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
2To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, 3da Filibus, da Bartalamawas, da Toma, da Matiyu mai karɓar haraji, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza, 4da Saminu Bakan'ane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.
Yesu Ya Aiki Sha Biyu Ɗin
(Mar 6.7-13; Luk 9.1-6)
5Su sha biyun nan ne Yesu ya aika, ya yi musu umarni, ya ce, “Kada ku shiga ƙasar al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa. 6Sai dai ku je wurin batattun tumakin jama'ar Isra'ila, Irm 7kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, ‘Mulkin Sama ya kusato.’ 8Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta. 9Kada ku riƙi kuɗin zinariya, ko na azurfa, ko na tagulla a ɗamararku, 10#1Kor 9.14; 1Tim 5.18 kada kuma ku ɗauki burgami a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci hakkinsa. 11Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma baƙunce shi har ku tashi. 12In za ku shiga gidan ku ce, ‘Salama alaiku.’ 13In gidan na kirki ne, salamarku tă tabbata a gare shi. In kuwa ba na kirki ba ne, to, tă komo muku. 14#A.M 13.51 Kowa kuma ya ƙi yin na'am da ku, ko kuwa ya ƙi sauraron maganarku, da fitarku gidan ko garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku. 15#Mat 11.24; Far 19.24-28#Luk 10.4-12 Hakika, ina gaya muku, a Ranar Shari'a za a fi haƙurce wa ƙasar Saduma da ta Gwamrata a kan garin nan.”
Tsanani Mai Zuwa
(Mar 13.9-13; Luk 12.11-12; Luk 21.12-19)
16 # Luk 10.3 “Ga shi, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai. Don haka sai ku zama masu azanci kamar macizai, da kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi. 17#Mar 13.9-11; Luk 12.11,12; 21.12-15 Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi muku bulala a majami'arsu. 18Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al'ummai kuma. 19A lokacin da suka ba da ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku faɗa, domin za a ba ku abin da za ku faɗa a lokacin. 20Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku. 21#Mar 13.12; Luk 21.16 'Dan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu, har su sa a kashe su. 22#Mat 24.9; Mar 13.13; Luk 21.17; Mat 24.13; Mar 13.13 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu. 23In sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Gaskiya, ina gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Ɗan Mutum zai zo.
24 # Luk 6.40; Yah 13.16; 15.20 “Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba ya fin ubangijinsa. 25#Mat 9.34; 12.24; Mar 3.22; Luk 11.15 Ya isa wa almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira maigida Ba'alzabul, to, mutanen gidansa kuma fa?”
Wanda Za a Ji Tsoro
(Luk 12.2-7)
26 # Mar 4.22; Luk 8.17 “Don haka kada ku ji tsoronsu, domin ba abin da yake a rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba. 27Abin da nake gaya muku a asirce, ku faɗa a sarari. Abin da kuma kuka ji a raɗe, ku yi shelarsa daga kan soraye. 28Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta. 29Ashe, ba gwara biyu ne kobo ba? Ba kuwa ɗayarsu da za ta mutu, ba da yardar Ubanku ba. 30Ai, ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake. 31Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”
Bayyana Yarda da Almasihu gaban Mutane
(Luk 12.8-9)
32“Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin Sama. 33#2Tim 2.12 Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubanmu da yake cikin Sama.”
Ban Kawo Salama Ba, Sai Takobi
(Luk 12.51-53; 14.26-27)
34“Kada dai ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. A'a, ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi. 35#Mika 7.6 Domin na zo ne in haɗa mutum da ubansa gāba, 'ya da uwatata, matar ɗa kuma da surukarta. 36Zai zamana kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa. 37Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. 38#Mat 16.24; Mar 8.34; Luk 9.23 Wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba. 39#Mat 16.25; Mar 8.35; Luk 9.24; 17.33; Yah 12.25 Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, adana shi yake yi.”
Ayyukan Lada
(Mar 9.41)
40 # Luk 10.16; Yah 13.20; Mar 9.37; Luk 9.48 “Wanda ya yi na'am da ku, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni. 41Wanda ya yi na'am da wani annabi domin shi annabi ne, zai sami ladar annabi. Wanda kuma ya yi na'am da adali domin shi adali ne, zai sami ladar adali. 42Kowa ya ba ɗaya daga cikin 'yan yaran nan, ko da moɗa guda ta baƙin ruwa, kan shi almajirina ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa ladarsa ba.”

Currently Selected:

Mat 10: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in