YouVersion Logo
Search Icon

Yun 1

1
Yunusa Ya Yi Gudun Ubangiji
1 # 2Sar 14.25 Ana nan sai Ubangiji ya yi magana da Yunusa, ɗan Amittai, ya ce, 2“Ka tashi ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka faɗakar da su, gama na ga irin muguntarsu.” 3Amma maimakon Yunusa yă tafi, sai ya gudu daga wurin Ubangiji zuwa Tarshish. Ya tafi Yafa, nan ya sami jirgin ruwa yana gab da tashi zuwa Tarshish, ya kuwa biya kuɗinsa, ya shiga tare da masu jirgin zuwa can don yă tsere wa Ubangiji.
4Amma Ubangiji ya aika da iska mai ƙarfi a tekun, hadirin ya tsananta ƙwarai har jirgin yana bakin farfashewa. 5Dukan matuƙan jirgin suka firgita, sai kowannensu ya shiga roƙon allahnsa. Suka yi ta jefar da kayan da suke cikin jirgin a ruwa don su sami sauƙi. Yunusa kuwa yana can cikin jirgi, a kwance, yana ta sharar barci.
6Can shugaban jirgin ya iske shi, ya ce masa, “Me ya sa kake barci? Tashi ka roƙi allahnka, watakila allahnka zai ji tausayinmu, yă cece mu.”
7Matuƙan jirgin kuwa suka ce wa junansu, “To, bari mu jefa kuri'a mu gani ko alhakin wane ne ya jawo mana wannan bala'i da muke ciki.” Sai suka jefa kuri'a, kuri'ar kuwa ta fāɗa a kan Yunusa. 8Suka ce masa, “Ka faɗa mana, laifin wane ne ya jawo mana wannan masifa? Mene ne aikinka? Daga ina ka fito? Daga wace al'umma kake?”
9Sai Yunusa ya ce, “Ni Ba'ibrane ne, ina bin Ubangiji Allah na Sama, wanda ya yi teku da ƙasa.”
10Sai matuƙan jirgin suka tsorata ƙwarai, suka ce masa, “Wane irin mugun abu ne ka aikata haka?” Sun sani ya gudu ne daga wurin Ubangiji, gama ya riga ya faɗa musu. 11Hadirin kuwa sai ƙaruwa yake ta yi. Matuƙan jirgin kuwa suka ce masa, “Me za mu yi maka domin tekun ya lafa?”
12Yunusa ya ce, “Sai ku ɗauke ni ku jefa ni cikin tekun, sa'an nan hadirin zai lafa. Gama na sani saboda ni ne wannan hadiri mai banrazana ya auko muku.”
13Matuƙan jirgin kuwa suka yi ta tuƙi da iyakar ƙarfinsu don su kai gaɓa, amma suka kāsa domin hadirin yana ta ƙaruwa. 14Suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Ya Ubangiji, muna roƙonka kada ka bar mu mu halaka saboda ran mutumin nan, kada ka yi mana hukuncin masu kisankai, gama kai ne, ya Ubangiji, ka yi abin da ya gamshe ka.” 15Sai suka ɗauki Yunusa suka jefa shi cikin teku, nan take teku ta lafa. 16Sai matuƙan jirgin suka ji tsoron Ubangiji ƙwarai, har suka ba da sadaka, suka kuma yi wa'adi ga Ubangiji.
17 # Mat 12.40 Ubangiji kuwa ya umarci wani babban kifi ya haɗiye Yunusa. Yunusa kuwa ya yi yini uku da dare uku a cikin cikin kifin.

Currently Selected:

Yun 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in